Atiku ya goyi bayan tafiyar ‘Tinubu Must Go’

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Tsohon mataimakin Shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya bayyana goyon bayansa ga ƙungiyar ‘Tinubu Must Go’ (TMG), yana mai cewa yunƙurin na nuna ƙudurin ’yan Nijeriya na ceto ƙasar.

Atiku, wanda shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, ya bayyana hakan ne bayan da ya karɓi bakuncin ɗaya daga cikin waɗanda suka assasa ƙungiyar, Abba Hikima, a gidansa da ke Abuja.

A cewar wata sanarwa da aka fitar ranar Litinin, Atiku ya ce abin da ya fi burge shi shi ne yadda ƙungiyar ke jan hankalin jama’a da kuma ƙara wayar da kan al’umma.

ƙungiyar Tinubu Must Go ta fara samun karɓuwa a lokacin zanga-zangar Ranar Dimokuraɗiyya ta 12 ga Yuni, 2026, inda masu zanga-zangar a wasu birane ciki har da Legas da Abuja suka rika rera taken ƙungiyar, tare da neman ɗaukar mataki kan matsalar tsaro da sace malamai da ɗaliban makaranta a Ogbomoso, Jihar Oyo.

Daga baya, a tsakiyar watan Satumba, ƙungiyar ta zama wani tsari mai ɗorewa, inda masu shirya ta suka bayyana cewa ba ta da alaƙa da wata jam’iyya, kuma tana mai da hankali ne kan wayar da kan jama’a da kuma gina turjiya ga shirin Shugaba Bola Tinubu na neman wa’adi na biyu.

Haka kuma, ƙungiyar ta gudanar da wani zaɓen ra’ayin jama’a na intanet na tsawon sa’o’i 24 tsakanin 24 zuwa 25 ga Satumba, domin gano ɗan takarar shugaban ƙasa na ’yan adawa da masu zaɓe za su fi bai wa ƙuri’a.

Atiku ya ce zaɓen ra’ayin jama’ar ya samu halartar mutane 109,799, inda ya ce shi ne ya samu kaso mafi yawa na ƙuri’un.

Ya ce, “Abin da ya ƙara ƙarfafa mini gwiwa shi ne yadda jama’a suka shiga cikin wannan aiki, inda takararmu ta samu kashi 73.6 cikin 100 na ƙuri’un, yayin da ADC ta zama jam’iyyar da aka fi so.”

Sai dai Atiku ya ce abin da ya fi muhimmanci ba sakamakon zaɓen ra’ayin jama’ar ba ne, illa saƙon da yake isarwa na cewa akwai ƙarin ’yan Nijeriya da ke son sauyi.

By ukarofi

Leave a Reply