Pantami ya lashe sabon zaɓen fidda gwani na PDP a Gombe

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ya lashe sabon zaɓen fidda gwani na Jam’iyyar PDP na neman tikitin takarar Gwamnan Jihar Gombe a zaɓen 2027.

Pantami ya samu nasara a zaɓen da aka gudanar a faɗin ƙananan hukumomi 11 na jihar, inda ya samu kuri’u 2,054, yayin da Khamisu Ahmed Mailantarki ya samu kuri’u 389, sannan Usman Aliyu Garry ya samu kuri’u 112. An sanar da sakamakon ne a sakatariyar PDP ta jihar Gombe.

An gudanar da sabon zaɓen ne a ranar Talata, 29 ga Satumba, 2026, bayan Babbar Kotun Tarayya da ke Gombe ta soke zaɓen fidda gwani na farko da ya samar da Pantami a matsayin ɗan takarar PDP na gwamnan jihar a zaɓen 2027.

A ranar 24 ga Satumba, Mai Shari’a Amina Aliyu Mohammed ta umarci PDP da ta sake gudanar da zaɓen fidda gwani cikin kwanaki 30, bayan da Khamisu Mailantarki da Usman Aliyu Garry suka ƙalubalanci tsarin da aka bi wajen fitar da Pantami a matsayin ɗan takarar jam’iyyar.

Kotun ta bayyana cewa tsarin da aka bi wajen gudanar da zaɓen farko bai yi daidai da wasu ƙa’idojin cikin gida na jam’iyyar da kuma tanade-tanaden dokokin zaɓe ba. Sai dai kotun ba ta amince da buƙatar da aka gabatar na cire Pantami daga cikin ’yan PDP ba, ko kuma hana shi kasancewa ɗan jam’iyyar.

Bayan hukuncin kotun, PDP ta sanya ranar 29 ga Satumba domin gudanar da sabon zaɓen, inda ta amince da Pantami, Mailantarki da Garry a matsayin ’yan takarar da za su fafata.

Sabon zaɓen ya gudana a rumfunan siyasa da ke faɗin ƙananan hukumomi 11 da kuma mazabu 114 na jihar, inda ’yan takarar uku suka fafata domin samun tikitin jam’iyyar na zaɓen gwamnan Gombe na 2027.

Da sanar da sakamakon, Shugaban Kwamitin Zaɓen Fidda Gwani na PDP daga hedikwatar jam’iyyar ta ƙasa, Johnbull Shekarau, ya bayyana Pantami a matsayin wanda ya samu nasara.

Wannan nasara ta sake bai wa Pantami tikitin tsayawa takarar gwamnan Gombe a ƙarƙashin PDP, bayan da zaɓen farko da ya ba shi tikitin ya shiga ƙalubalen shari’a, lamarin da ya kai ga soke shi da kotu da kuma umartar jam’iyyar ta sake gudanar da zaɓen.

Pantami, wanda ya taɓa riƙe muƙamin Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani daga 2019 zuwa 2023, ya koma PDP ne bayan ya janye daga neman tikitin APC na takarar gwamnan Gombe.

By ukarofi

Leave a Reply