Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Jihar Kano ta kasa bayyana adadin kuɗaɗen shiga da ƙananan hukumominta 44 suka samar aƙalla sau uku cikin rahotannin baya-bayan nan na Hukumar ƙididdiga ta ƙasa (NBS), duk da cewa kuɗaɗen shiga na cikin gida na gwamnatin jihar sun kusan ninka sau uku tsakanin shekarar 2023 zuwa 2025.
Wani kwatanci tsakanin bayanan NBS da na gwamnatin jihar ya nuna hakan. Bayanan NBS sun nuna cewa Kano na cikin jihohi 16 da suka bayar da rahoton cewa ƙananan hukumominsu ba su samu ko sisin kwabo na kuɗaɗen shiga a shekarar 2023 ba.
Sauran jihohin sun haɗa da Ribas, Delta, Enugu, Anambra, Katsina, Filato, Nasarawa, Zamfara, Neja, Bayelsa, Benuwe, Sakkwato, Adamawa, Kebbi da Yobe.
A waccan shekarar, ƙananan hukumomin jihohi 20 ne kawai suka bayar da rahoton samun jimillar Naira biliyan 37.05 a matsayin kuɗaɗen shiga a faɗin aasar. Wannan ya ragu daga Naira biliyan 48.7 da jihohi 29 suka samu a shekarar 2022, inda Oyo, Legas da Jigawa suka kasance jihohin da ƙananan hukumominsu suka fi samun kuɗaɗen shiga, ba tare da Kano ba.
Kano ta sake kasancewa cikin jihohin da ba su bayar da rahoton kuɗaɗen shiga na ƙananan hukumomi ba a shekarar 2025, lokacin da jihohi 21 suka bayar da rahoton jimillar Naira biliyan 65.82.
Wannan matsala ba ta tsaya ga Kano kaɗai ba. A cewar NBS, jihar Katsina ma ta bayar da rahoton cewa ba ta samu kuɗaɗen shiga daga ƙananan hukumominta ba a shekarun 2022 da 2023. Sai dai Kaduna ta bayar da rahoton samun Naira miliyan 382.22 daga ƙananan hukumominta a 2023, abin da ya sanya ta a matsayi na 12 cikin jihohi 20 da suka gabatar da bayanan.
Adadin Kaduna ya yi nisa da na Legas da ya kai Naira biliyan 10.49, da Ebonyi wadda ta samu Naira biliyan 6.13.
Kuɗaɗen shiga na Kano sun ninka:
Abin da ya bambanta Kano da wasu jihohin Arewa shi ne yadda take samun aarin kuɗaɗen shiga a matakin gwamnati ta jiha. Bayanan Hukumar Tara Kuɗaɗen Shiga ta Jihar Kano (KIRS) sun nuna cewa kuɗaɗen shiga na cikin gida na jihar sun tashi daga Naira biliyan 37.39 a shekarar 2023 zuwa Naira biliyan 74.77 a 2024, wato ƙarin kashi 100 cikin 100. A shekarar 2025 kuma, adadin ya ƙara tashi zuwa kusan Naira biliyan 102.
Wannan ƙaruwa ta sanya Kano a matsayi na tara a faɗin ƙasar, sannan ta zama jihar da ta fi kowacce a Arewacin Nijeriya samun kuɗaɗen shiga na cikin gida, a cewar Shugaban KIRS, Zaid Abubakar. Ya ce, hakan ya sauya matsayin Kano daga matsayi na kusan 30 da ta taɓa kasancewa a baya. Hukumar ta kuma sanya wa kanta burin tara Naira biliyan 200 a shekarar 2026.
A gefe guda, Kaduna wadda a baya ta kasance kan gaba a Arewa wajen tara kuɗaɗen shiga na cikin gida, ta tattara Naira biliyan 58 a 2022, Naira biliyan 62.48 a 2023 da kuma Naira biliyan 71 a 2024, a cewar Hukumar Tara Kuɗaɗen Shiga ta Jihar Kaduna.
Adadin Kano na kusan Naira biliyan 102 a 2025 ya fi na Kaduna da aka bayyana na cikakkiyar shekarar baya, duk da cewa Kaduna na bayar da rahoton kuɗaɗen shiga na ƙananan hukumominta ga NBS, yayin da Kano ba ta yin hakan.
