Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Ministan Kasafi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki, Atiku Bagudu, ya ce tattalin arzikin Nijeriya har yanzu bai kai bunƙasar da zai iya biyan manyan buƙatun cigaban ƙasar ba.
Ministan ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a Majalisar ƙasa, inda ya ce idan Nijeriya ba ta ɗauki matakan da suka dace wajen bunƙasa tattalin arzikinta ba, ƙasar za ta ci gaba da kasa cimma muradun da ’yan ƙasa ke sa ran gwamnati za ta cika.
Bagudu ya bayyana hakan ne yayin wani taron horas da ’yan jarida kan harkokin kasafin kuɗi, inda ya ce Nijeriya na daga cikin ƙasashen 10 mafi yawan al’umma a duniya da ke da mafi ƙarancin kasafin kuɗi. Ya danganta wannan yanayi, a wani ɓangare, da ƙarancin yawan kuɗaɗen shiga da gwamnati ke samu idan aka kwatanta da girman tattalin arzikin ƙasar.
“Wannan tattalin arziki ƙarami ne, kuma zai ci gaba da bai wa mutane taƙaici matuƙar ba mu gyara shi yadda ya kamata ba,” inji shi.
Ministan ya kwatanta Nijeriya da wasu ƙasashe masu yawan jama’a makamancin nata, inda ya kawo Pakistan da Brazil a matsayin misalai. Ya ce duk da cewa kasafin kuɗin Pakistan ya kai kusan dala biliyan 67, Brazil ce ta fi zama ma’aunin kwatance ga Nijeriya, saboda kamanceceniya wajen yawan jama’a da kuma tsarin mulkin tarayya.
A cewarsa, kasafin kuɗin gwamnatin tarayyar Brazil na shekarar 2025 ya fi na Nijeriya girma da aƙalla sau 25. Bagudu ya tambayi yadda Nijeriya za ta iya cimma irin matakan ci gaba da ƙasashe irin Brazil ke samu, alhali kuwa tana da ƙarancin albarkatun kuɗi sosai.
“Shin ina tsammanin zan cimma irin sakamakon da Brazil ke samu da kasafin kuɗi mafi ƙanƙanta sosai? Shin buƙatun da muke magana a kansu ba su wanzu ba ne? Na yi imanin cewa suna nan,” inji ministan.
Ya ƙara da cewa Gwamnatin Tarayya na aiki domin gina tattalin arzikin Nijeriya zuwa darajar dala tiriliyan ɗaya, daidai da manyan manufofin ci gaban ƙasar na dogon lokaci.
Sai dai ya ce cimma wannan buri zai buƙaci gwamnati ta ƙara ƙoƙarin tattara kuɗaɗen shiga, jawo ƙarin zuba jari, sannan ta nemi bashi idan buƙata ta taso, muddin hakan yana samun amincewar jama’a.
Da yake magana kan tsarin kasafin kuɗin ƙasa, Bagudu ya ce kasafin kuɗi sakamakon tattaunawa ne tsakanin bangaren zartarwa, jama’a da kuma Majalisar ƙasa, wadda Kundin Tsarin Mulki ya ba wa ikon amincewa da yadda za a kashe kuɗaɗen gwamnati. Ya kuma buƙaci kafafen yaɗa labarai su taimaka wa jama’a wajen fahimtar dalilan da suka sa aka ware kuɗaɗe ga wasu ayyuka a cikin kasafin kuɗi, tare da tabbatar da sahihancin abubuwan da ake zargi kafin a ayyana su a matsayin abubuwan da aka shigar ba bisa ƙa’ida ba.
Ministan ya ce akwai lokutan da wasu tanade-tanaden kasafi da aka fara kallonsu da shakku daga baya aka gano cewa suna da alaƙa da ainihin buƙatun al’ummomin da abin ya shafa.
Saboda haka, ya shawarci ’yan jarida da su binciki duk wani tanadin kasafi da ke da shakku, amma su tabbatar da gaskiyar bayanan da suka danganci abin kafin su kai ga yanke hukunci ko wallafa rahoto a kansa.
Bagudu ya kuma yi gargaɗin cewa bai kamata a auna nasarar aiwatar da kasafin kuɗi ta hanyar kallon kuɗaɗen ayyukan raya ƙasa kaɗai ba. Ya ce kuɗaɗen gudanar da gwamnati, albashin ma’aikata, tsaro da kuma biyan basussuka duk muhimman abubuwa ne da ake buƙata domin gwamnati ta ci gaba da gudanar da ayyukanta.
Ministan ya yi kira ga Majalisar ƙasa da kafafen yaɗa labarai da su ci gaba da haɗin gwiwa wajen ƙarfafa gaskiya, riƙon amana da kuma fahimtar jama’a game da yadda tsarin kasafin kuɗin Nijeriya ke gudana.
