‘Yan bindiga sun halaka mutum biyu bayan kai farmaki a wajen haƙar ma’adinai a Filato

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Rahotanni daga Jihar Filato a Arewa ta Tsakiyan Nijeriya sun bayyana cewa wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun ƙaddamar da wani hari a wajen haƙar ma’adinai da ke yankin Kuru Jenta na Gundumar Haipang a Ƙaramar Hukumar Barikin Ladi a daren wayewar Asabar, inda suka halaka mutane biyu.

Sakataren Ƙungiyar Matasan Ƙabilar Berom (BYM), Rwang Tengwong wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin a wata takarda a ranar Asabar, ya ce al’amarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:30 na dare a lokacin da mutanen suke bakin aiki.

Tengwong ya bayyana harin a matsayin abin takaici, wanda ya auku ƙasa da mako guda da wasu ‘yan bindiga suka halaka mutum biyu a wani gurin haƙar ma’adinai da ke ƙauyen Rakum a Ƙaramar Hukumar Jos ta Kudu. Akan haka ne ya yi kira ga hukumomin tsaro da su gudanar da bincike kan al’amarin tare da gano masu hannu a ciki da gurfanar da su domin su fuskanci hukuncin doka.

Kakakin na BYN ya kuma gargaɗi mazauna musamman masu aikin haƙar ma’adinai akan gudanar da aikin a lokacin dare, yana mai kira a gare su da su kasance masu lura da sanya ido tare da bai wa jami’an hukumomin tsaro haɗin kai akan matakan da gwamnatin ta samar kan halin tsaron yankunansu.

Kazalika, ya kuma bayyana kaɗuwarsa musamman ganin yadda al’amarin ya auku a daidai lokacin da gwamnatin jihar ta sanya dokar kulle a ƙananan hukumomi uku ciki har da Barikin Ladi, inda aka samu aukuwar lamarin, yana mai kira ga mazauna da su riƙa kiyaye sa’o’in da dokar kullen ta shafa, zama masu lura da kauce wa dukkan wani abin da zai jefa su ciki haɗarin tsaro, yayin da kuma suke nazari kan halin tsaro a yankunansu.

By Babaji

Leave a Reply