
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar kula da Harkokin Ƙwallon Ƙafa ta Ƙasa NFF, ta aike da saƙon gargaɗi ga alƙalan wasa da ke jagoranta wasannin Premier League ta Nijeriya (NPFL), inda ta ce wajibi ne a riƙa tabbatar da adalci da daidai yayin alƙalanci a baki ɗaya wasannin kakar.
A wata wasiƙa da ta aike wa ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na NPFL, kwamitin ci-gaban harkar alƙalanci ta hannun Mohammed Ameenu, NFF ta ce wannan gargaɗi ya zama wajibi domin bayar da kariya ga nasarorin da aka samu a harkar alkalancin wasanni tun bayan fara gasar makonni shida da suka gabata.
Hukumar ta ce tana sane da cewa alƙalan sun yi ƙoƙari a ‘yan makonnin nan wajen gudanar da ayyukansu, amma duk da haka ta gano wasu kurakurai, ciki har da rashin aiwatar da wasu dokokin wasa, waɗanda ta ga sun dace ta ankarar da su akansu. Don haka ta umarci jami’an wasa da su riƙa kiyaye gaskiya da adalci da kuma aiwatar da dokokin wasanni na Game 2026 a tsari na daidai ta yadda za su gamsar da masu ruwa da tsaki a fannin ƙwallo.
Kazalika, ta kuma yi gargaɗin cewa dukkan wani alƙali da aka samu da saɓa wa dokoki ko yin dameji ga martabar gasar, zai iya fuskantar hukuncin kora tare da damƙa shi ga hukumomin tsaro domin gurfanarwa.
Ana ganin wannan sanarwa a matsayin ɓangare na ƙoƙarin tabbatar da cewa ‘yan wasa su ke sa iko akan sakamakon wasannin ba kurakuran jami’an alƙalanci ba.
