
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Rundunar ‘Yan sanda a Jihar Imo, ta ce ta gano wajen da aka kai ‘yan hidimar ƙasa (NYSC) su kusan 19 da wasu ‘yan bindiga suka yi awon-gaba da su a jihar. Kwamishinan ‘yan sandan, Audu Bosso ne ya bayyana haka yayin ganawa da manema labarai a ranar Asabar.
An ga wani faifan bidiyo da ya karaɗe kafafen sada zumunta da ke nuna shugaban ‘yan sandan yana jawabin. Da fari, rahotanni sun bayyana cewa an sace ‘yan hidimar ƙasar ne da misalin ƙarfe 6:30 na safiyar ranar Alhamis akan hanyar Owerri zuwa Onitsha ta yankin Umunoha a Jihar Imo.
An ruwaito cewa al’amarin ya auku ne a lokacin da ‘yan NYSCn suke kan hanyar tafiya zuwa sansanonin karɓar horo daga Ibadan, Jihar Oyo zuwa jihohin Abia da Akwa-Ibom. ‘Yan sandan sun ce an yi nasarar mutum 10 daga cikinsu bayan ƙaddamar da wani atisayen jami’an rundunar da na wasu hukumomin tsaro, yayin da aka tantance ainihin adadin waɗanda suke hannun ‘yan bindigar.
Kwamishinan ya ce, jami’ansu sun yi amfani da jirage maras matuƙi ne a ranar Juma’a wajen gano maɓoyar ‘yan bindigar bayan jami’an tsaro sun farauce su. Ya bayyana cewa, jami’an tsaro suna yin kaffa-kaffa ne wajen ƙaddamar da hari a yankin sakamakon bayanan sirri sun nuna cewa an dasa wasu ababen fashewa a hanyar da za ta kai su zuwa wajen.
A cewarsa suna cigaba nazari tare da amfani da dabarun aiki wajen bin hanyoyin da suka dace domin samun nasarar ceto sauran waɗanda suke tsare a hannun a hannun ‘yan bindigar. Har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoto, babu wata daba ko ƙungiya da ta yi iƙirarin alhaki kan al’amarin.
