
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
‘Yan bindigar da suka sace ‘yan hidimar ƙasa na NYSC su guda 20 a kudancin Nijeriya sun sanar da rage adadin kuɗin fansar da suka buƙaci a biya da fari domin sako su, daga Naira miliyan 50 zuwa Naira miliyan 5 ga kowannensu, lamarin da ya dawo da ainihin kuɗin zuwa miliyan N100.
Tun a ranar Juma’a ne dai masu garkuwar suka bayar da wa’adin kwana guda domin a biya miliyan N50 ɗin da suka buƙata da fari ga kowane ɗaya daga cikin ‘yan hidimar, inda ake tsammanin wa’adin ya ƙare a yau Lahadi.
Ɗaya daga cikin iyayen ‘yan hidimar mai suna Alimot Akande yayin wata hira ta kiran waya, ta shaida wa ‘yan jarida cewa an rage kuɗin fansar zuwa Naira miliyan 5 ga kowanne. Ta ce, sun samu bayanin haka ne bayan ‘yan bindigar sun tattauna da iyayen waɗanda suka sacen da wayoyin hannunsu.
Uwar ta kuma bayyana cewa, ana cin zarafin ‘ya’yansu ta hanyar lakaɗa musu duka a hannun ‘yan bindigar ba tare da tausayawa ba domin sanya dangi su gaggauta haɗa kuɗin fansar su kai musu ko kuma su fuskanci wata matsala daban.
Da fari, jimillar abin da ‘yan bindigar suka buƙaci a biya shi ne Naira biliyan ɗaya ga ‘yan hidima 20, wato miliyan N50 ga kowanne, inda a yanzu kuma aka dawo da shi miliyan N100.
A ranar Alhamis ne dai aka yi awon-gaba da ‘yan hidimar su 20 a wani yanki na Jihar Imo yayin da suka taho daga Ibadan, Jihar Oyo domin zuwa sansanonin karɓar horo a jihohin Abia da Akwa-Ibom. Saidai daga bisani, rundunar ‘yan sandan Imo ta yi iƙirarin ceto mutum 10 daga ciki a ranar Asabar.
