WAEC ta ƙara ba wani ɗan Nijeriya babban muƙami

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Majalisar Shirya Jarrabawa a Yammacin Afirka (WAEC) ta naɗa Mista Suleiman Ɗanlami Kum a matsayin sabon Shugaban Reshenta na Nijeriya, inda ya maye gurbin Dakta Amos Josiah Dangut.

Kum, wanda ƙwararren jami’in gudanar da harkokin jarrabawa ne, ya fara aiki da WAEC ne tun a shekarar 1998 a matsayin Mataimakin Rajistara na II. An haife shi a ranar 16 ga watan Oktoban 1970, kuma ainihinsa ɗan Ƙaramar Hukumar Langtang ta Arewa ne daga Jihar Filato.

Ya yi digirinsa na farko a Tsangayar Noma a Fannin Kiwon Dabbobi na Jami’ar Noma da ke Makurɗi a Jihar Benuwai a shekarar 1992, kana ya Difulomar bayan digiri a fannin Ilimi a Jami’ar National Open University (NOUN) a 2025. A yanzu yana ƙoƙarin kammala digiri na biyu a fannin a NOUN.

A matsayinsa na ƙwararren ma’aikaci da ya yi mata hidima a jihohi daban-daban, WAEC ta bayyana shi a matsayin jami’i mai mutunta aiki, jajircewa da ƙoƙarin sauke nauyin da aka ɗora masa, tana mai masa fatan riƙe sabon muƙamin nasa bisa gaskiya da adalci.

Gabanin wannan muƙami Mista Kum shi ne Mataimakin Rajistara a Ofishin Shugaban WAEC reshen Nijeriya.

By Babaji

Leave a Reply