Shettima ya ƙaddamar da asusun tallafin zuba jari ga mata 40,000 a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Fiye da mata 40,000 a Jihar Katsina za su amfana da tallafin jari domin faɗaɗa sana’o’insu da ƙarfafa tattalin arzikinsu

Mataimakin shugaban ƙasar Najeriya, Sanata Kashim Shettima, ne ya ƙaddamar da rabon asusun zuba jari na al’umma (CIF) ƙarƙashin shirin Nigeria for Women Programme Scale-Up (NFWP-SU) a filin wasa na Muhammadu Dikko da ke Katsina.

Ya ce shirin wani jari ne ga ƙwarewa, sana’o’i da damar tattalin arzikin mata.

Shettima ya ce sama da mata 40,000 ne za su samu jari bayan sun cika sharuɗan cancanta tare da nuna ƙwazo a tsarin ajiyarsu da ayyukan ƙungiyoyinsu. Ya kuma yaba wa Gwamna Dikko Umar Raɗɗa kan fifita mata da iyalan da ke buƙatar tallafi, tare da jaddada cewa nasarar shirin za ta kasance ne idan sana’o’in mata sun ƙaru, kuɗin shiga na iyalai ya inganta, an samu ƙarin ayyukan yi, kuma mata sun samu damar yanke shawara kan harkokin tattalin arzikinsu.

Mataimakin shugaban ƙasar ya kuma buƙaci waɗanda za su amfana su ci gaba da bin tsarin ajiya, adana bayanan harkokinsu da kuma haɗin kai da suka ba su damar samun tallafin. Ya kuma yi kira ga masu gudanar da asusun da su tabbatar da gaskiya, adalci, cikakken bayanan rabon kuɗi da kuma riƙon amana a dukkan matakan shirin.

Da yake jawabi, Gwamna Raɗɗa ya ce ƙarfafa tattalin arzikin mata na daga cikin muhimman manufofin ajandarsa ta Building Your Future. Ya ce jihar Katsina ta samar da ƙarin kuɗaɗe domin haɗawa da tallafin Bankin Duniya, abin da ya taimaka wajen faɗaɗa shirin daga ƙananan hukumomi shida zuwa dukkan ƙananan hukumomi 34 na jihar. Ya bayyana cewa asusun zai taimaka wa ƙungiyoyin mata wajen kafa sabbin sana’o’i da faɗaɗa waɗanda suke da su.

Gwamnan ya jaddada cewa ƙaddamarwar ba ita ce ƙarshen rabon kuɗin ba, domin za a ci gaba da rabawa ƙungiyoyin da ba su samu tallafi a ranar ba a matakai daban-daban.

Ya kuma yi kira ga Bankin Duniya da sauran abokan hulɗar ci gaba da ƙara tallafin kuɗi da na ƙwarewa domin a kai shirin ga ƙarin mata, musamman waɗanda ke cikin wuraren da ba sa samun isasshen tallafi. Ya kuma bayyana cewa shirin ya haɗa da mata masu matsalar ji waɗanda suka kafa ƙungiyoyinsu na musamman.

A nasa jawabin, wakilin Bankin Duniya, Matthew Verghis, ya ce saka jari a cikin mata na taimakawa wajen bunƙasa tattalin arzikin Najeriya. Ya bayyana cewa shirin NFWP-SU na dala miliyan 540 ana aiwatar da shi a jihohi 32, kuma yana da nufin tallafa wa mata miliyan biyar kai tsaye. Ya ce mata da ke cikin shirin sun riga sun tara sama da Naira biliyan 20 a matsayin ajiyarsu.

A nata ɓangaren, kwamishiniyar harkokin mata ta Katsina, Hajiya Aisha Aminu Malumfashi, ta ce an kafa ƙungiyoyin mata sama da 2,393 a Katsina da Daura, yayin da aka tara sama da Naira miliyan 310.

Ta buƙaci waɗanda suka samu tallafin su yi amfani da kuɗin wajen bunƙasa sana’o’insu da inganta rayuwar iyalansu da al’ummominsu.

By ukarofi

Leave a Reply