Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Rundunar ’yan sandan Jihar Kano ta gayyaci matashin ɗan siyasar nan Hon. Aminu Abdullahi Warkal domin gudanar da bincike bisa zarginsa da nuna bindiga a fili yayin wani taron siyasa.
Arewa Updates ta rawaito cewa, wannan na cikin sanarwar da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar a ranar Litinin, 5 ga Oktoba, 2026.
Sanarwar ta ce rundunar ta ga wani bidiyo a kafafen sada zumunta, inda aka ga Warkal yana nuna wani makami da ake zargin bindiga ce, lamarin da ya sa kwamishinan ’yan sandan Jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ya bayar da umarnin gayyatarsa zuwa hedikwatar rundunar da ke Bompai.
Kazalika, rundunar ta ce Warkal yana sashen binciken sirri na rundunar, CID, yayin da ake ci gaba da bincike domin tabbatar da zargin, tare da gargaɗin cewa ba za ta lamunci da nuna makaman da za su iya barazana ga zaman lafiya ba.
Kwamishinan ’yan sandan ya kuma buƙaci ’yan siyasa, magoya bayansu da sauran masu ruwa da tsaki su gudanar da harkokinsu cikin lumana tare da bin dokokin zaɓe, dokar mallakar makamai da sauran dokokin ƙasa.
