Kwamandan Hisbah na Jihar Katsina ya ajiye muƙaminsa

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Babban kwamandan hukumar Hisbah ta Jihar Katsina, Dr. Aminu Usman (Abu Ammar), ya sanar da yin murabus daga muƙamin sa.

Ya bayyana hakan ne a wata wasiƙa ɗauke da sa hannun sa ya aike wa sakataren gwamnatin Jihar Katsina.

A wasiƙar da bai yi wani bayanin dalilin murabus ba, Dr. Aminu Usman ya gode wa Gwamna Dikko Umar Raɗɗa bisa amincewa da damar da ya ba shi na yi wa al’ummar jihar hidima. Ya ce ya yi farin cikin bayar da gudummawarsa wajen ci gaban jihar, zaman lafiya, tsaro da kyautata tarbiyyar al’umma, tare da yi wa gwamnan addu’ar samun nasara.

Manyan masu muƙami a gwamnatin Dikko Raɗɗa su huɗu kenan ɗaya bayan ɗaya suka ajiye muƙamin su.

Sai dai mutane na ganin taƙaddama a siyasa a tsakanin Gwamna Dikko Raɗɗa da mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin siyasa Ibrahim Masari ya taka rawa wajan halin da jam’iyar APC ta shiga a Jihar Katsina.

By ukarofi

Leave a Reply