‘Yan adawa ke siyasantar da harkar tsaro a Katsina – Mai Turaka

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Mataimaki na musamman ga gwamnan Katsina,Abdul’aziz Mai Turaka ya nuna takaici kan yadda wasu ‘yan adawa ke siyasantar da harkar tsaro a Jihar.

Mai Turaka wanda ya wakilci tsohon gwamnan Jihar Katsina Rt Hon Aminu Bello Masari a bikin bada tallafin kuɗi ga wasu ya’yan jam’iyar APC Katsina, yace yanayin tsaro ya inganta a Jihar idan aka waiwaya baya.

“Duk da cewa ana samun rahotannin hare hare a wasu ƙauyuka na wasu ƙananan hukumomin jihar, bai kai matakin da za ace gaba ɗaya babu tsaro a jihar,”Inji Mai Turaka.

“Su yan adawa da suke cewa babu tsaro a Jihar wane tallafi suka taɓa bai wa waɗanda hare haren ya rutsa da su a ƙananan hukumomin su,”yace.

Ya yaba wa haɗin gwiwa na gwamnatin tarayya da gwamnatin Katsina kan mataimakin da suka ɗaukar a cikin shekara uku wajen tabbatar da zaman lafiya a jihar.

Mai Turaka ya yi tsokaci kan zaɓen 2027 da yace ɗimbin aikace aikace na raya ƙasa da gwamnatin Dikko Raɗɗa ta aiwatar ya taimaka wajen tallar ‘yan takarar jam’iyar APC a Jihar.

Ya yi kira ga al’ummar jihar da su fito gaba ɗaya su zaɓi shugaban ƙasa Bola Tinubu da Gwamna Dikko Raɗɗa tare da saurin ‘yan takarar jam’iyar APC a Katsina.

Mai Turaka ya sanar da cewa tsohon gwamnan Jihar Aminu Bello Masari ya bada tallafin kuɗi Naira Miliyan 160 ga ya’yan jam’iyar su biyar a kowace gundumar a faɗin Jihar.

By ukarofi

Leave a Reply