Daga IBRAHIM HAMISU a Kano u
Jam’iyyar NDC a Jihar Kano ta bayyana fatan cewa hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) za ta dawo da sunan ɗan takararta na gwamna, Aminu Abdussalam Gwarzo, da mataimakinsa cikin jerin ’yan takarar zaɓen gwamnan jihar na 2027, idan aka gano cewa kuskure ne aka yi wajen cire sunayensu.
Shugaban jam’iyyar na jihar Kano, Hussaini Isah Mai Riga, ne ya bayyana hakan ranar Aluhamisu, inda ya ce jam’iyyar ta kai ƙorafinta ga uwar jam’iyya ta ƙasa, wadda ita ma ta miƙa batun ga INEC.
Kazalika, Mai Riga ya ce hukumar zaɓen ta yi alƙawarin gudanar da bincike kan cire sunayen ’yan takarar, yayin da jam’iyyar ke jiran sakamakon binciken.
“Mun rubuta wa uwar jam’iyyarmu ta ƙasa, ita kuma ta miƙa batun ga INEC. Hukumar ta ce za ta gudanar da bincike, kuma idan aka gano kuskure ne, za ta dawo da matsayin ’yan takararmu,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa a halin yanzu jam’iyyar na jiran martanin hukumar kafin ta yanke shawarar matakin da za ta ɗauka na gaba.
An cire sunayen Gwarzo da mataimakinsa daga jerin sunayen ’yan takarar gwamnan Kano na ƙarshe da INEC ta fitar, lamarin da ya jawo damuwa kan yiwuwar jam’iyyar ta shiga zaɓen gwamnan jihar na 2027.
Yanzu haka NDC na jiran sakamakon binciken hukumar zaɓen domin tabbatar da matsayin ’yan takararta da kuma sanin matakin da za ta ɗauka na gaba.
