Yayin da ’yan Nijeriya ke shirin tunkarar babban zaɓen shekarar 2027, barazanar tashin hankali da ka iya biyo bayan yaɗa labaran ƙarya ta sa Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, yin kira ga masu zaɓe da su guji duk wani abu da zai iya kawo cikas ga zaman lafiya da bin doka da oda a lokacin zaɓe da kuma bayansa.
A zaman Majalisar Dattawa na makon da ya gabata, shugaban majalisar dattawan ƙasar ya gargaɗi ’yan siyasa da sauran masu ruwa da tsaki da su guji duk wani mataki da zai iya kawo cikas ga sahihancin sakamakon zaɓe, musamman a wannan lokaci da makomar dimokuraɗiyyar Nijeriya ke buƙatar kulawa ta musamman.
Akpabio ya tunatar da ’yan Nijeriya cewa babu wata manufa ta siyasa da ta kai darajar ran ɗan ƙasa. Ya jaddada cewa wajibi ne dukkan masu ruwa da tsaki a harkokin zaɓe su haɗa kai wajen tabbatar da cewa an gudanar da zaɓe cikin lumana a duk faɗin ƙasar.
Damuwa kan yaɗuwar labaran ƙarya a kafafen sada zumunta, musamman waɗanda wasu mutane ke yaɗawa da gangan domin gurɓata sahihancin zaɓe, na ƙara sanya shakku kan yiwuwar gudanar da sahihin zaɓe a shekara mai zuwa.
Baya ga satar ƙuri’u, daba da tashe-tashen hankula da kuma amfani da kafafen yaɗa labarai wajen yi wa wata jam’iyya ko ɗan takara aiki, bunƙasar amfani da fasahar ƙirƙirarriyar basira ta AI ta sa ya zama wajibi Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC) ta rungumi sabbin fasahohin sadarwa da bayanai domin daƙile yaɗuwar ƙaryar da ka iya haddasa tashin hankali.
Da yake magana a wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja ranar Talata, kan shirye-shiryen hukumar ta INEC na gudanar da zaɓen ba tare da tangarɗa ba, Shugaban hukumar, Farfesa Joash Amupitan, ya bayyana cewa labaran ƙarya da aka samar ta amfani da basirar AI na daga cikin manyan barazanar da za su iya kawo cikas ga sahihancin zaɓen.
Ya yi kira ga kafafen yaɗa labarai da su kafa sassan tantance sahihancin bayanai a cikin hukumominsu, domin tabbatar da gaskiyar labarai kafin wallafa ko yaɗa su.
A ƙasar da rarrabuwar kawuna ta fuskar yanki, ƙabila da addini ta yi ƙarfi, amfani da bidiyoyin bogi masu kama da na gaskiya, kwaikwayon muryoyin mutane ta hanyar fasaha da kuma amfani da dandamalin asusu na bogi da ke aiki kai tsaye na iya tayar da zaune tsaye a lokacin zaɓe.
A cewar Amupitan, masu son haddasa tashin hankali a lokacin zaɓe na iya ƙirƙirar bidiyon bogi da ke nuna wani ɗan takara yana cin mutuncin wata al’umma, ko kuma kwaikwayon muryar jami’in zaɓe domin yaɗa sanarwar sakamakon zaɓen ƙarya. Irin waɗannan dabaru na iya haddasa rikici tare da raunana amincewar jama’a ga tsarin zaɓe.
Gargaɗin Akpabio ya ƙara samun muhimmanci idan aka yi la’akari da yadda fasahar AI ke ba da damar yaɗa ƙaryar da a baya sai an kashe kuɗi masu yawa ko amfani da ƙwararrun ma’aikatan kafafen yaɗa labarai kafin a iya samar da ita.
Daga cikin hanyoyin yaɗa labaran ƙarya da wannan fasaha ke samarwa akwai sautin murya da bidiyo na bogi da ake iya amfani da su wajen kwaikwayon muryar jami’in zaɓe yana sanar da sakamakon zaɓe na ƙarya.
Haka kuma, tsarin sarrafa bayanai na kafafen sada zumunta da ke amfani da basirar AI kan fifita abubuwan da ke jawo hankalin jama’a, ko da kuwa suna ƙunshe da ƙarya. Ana iya amfani da wannan damar wajen ƙirƙirar saƙonnin bogi da ke haddasa tsoro ko fushi, domin tayar da hankalin jama’a, jawo yawan masu kallon saƙonni da kuma yaɗa su cikin sauri.
Wannan tsari na iya sa masu amfani da kafafen sada zumunta su ria ganin bayanan da suka yi daidai da ra’ayoyinsu kawai, har su kulle kansu cikin wata duniyar bayanai da ba ta ba su damar tantance ra’ayoyin da suka saɓa da nasu.
A ƙasar da wasu ’yan ƙasa kan kasance a shirye su yarda da duk wani bayani da ya dace da muradunsu, tsarin yaɗa bayanai na cikin wani hali mai rauni, wanda ke sauƙaƙa wa masu son yin amfani da fasahar AI wajen yaɗa ƙarya.
ƙarancin ilimin amfani da fasahar zamani da kuma rashin amincewa da hukumomi na daga cikin abubuwan da ke sa wasu mutane kasa tantance sahihancin bayanan da suka wuce hankali kafin su yarda da su ko su yaɗa su.
Yayin da wasu ’yan ƙasa ke ƙara rasa amincewa da hukumomin gwamnati, kafafen yaɗa labarai da jami’an tsaro, suna komawa ga kafafen sada zumunta da sauran hanyoyin musayar saƙonni domin samun bayanai da yaɗa su.
Abin da ya fi muhimmanci a yanzu shi ne Hukumar Zaɓe ta ƙasa ta ɗauki matakan da suka dace wajen kare sahihancin zaɓen, ta hanyar tunkarar yaɗuwar labaran ƙarya da fasahar AI ke samarwa, musamman waɗanda masu son lashe zaɓe ko haddasa ruɗani a intanet ke yaɗawa.
Idan aka jira sai masu tantance sahihancin bayanai sun tabbatar da cewa wani saƙo ko bidiyo na bogi ne, akwai yiwuwar ƙaryar ta riga ta bazu a sassan ƙasar, ta haddasa rikici a tituna tare da ƙarfafa son zuciya da ake ɗauka a matsayin gaskiya.
Domin kauce wa wannan barazana, ya kamata gargaɗin Akpabio ya zama abin tunatarwa ga INEC da sauran hukumomin tsaro da ke da alhakin gudanar da zaɓe da tabbatar da tsaro, su ɗauki matakan kariya tun kafin matsala ta kunno kai. Rashin ɗaukar mataki a kan lokaci na iya jefa ƙasar cikin babban rikici wanda illolinsa za su yi wahalar ɗaukar nauyinsu.
Yanzu da babban jami’in zaɓe na ƙasa ya bayyana barazanar da labaran ƙarya ke haifarwa, wajibi ne INEC ta nuna aikinta a aikace, ta hanyar tunkarar ’yan siyasar da ke kallon zaɓe a matsayin fafatawar da sai wani ya faɗi kafin wani ya yi nasara.
Ya kamata hukumar ta samar da tsare-tsare da za su yi amfani da AI wajen gano ƙarya da daƙile yazuwarta, maimakon dogaro da matakan da ake ɗauka ne bayan an riga an yi ɓarna.
Haka kuma, ya kamata Majalisar Dokoki ta ƙasa, ƙarƙashin jagorancin Akpabio a Majalisar Dattawa, ta samar da dokoki da tsare-tsaren shari’a da za su taimaka wajen yaƙi da labaran ƙarya, ba tare da tauye ’yancin faɗar albarkacin baki ba.
A halin yanzu, dokokin da ake da su, ciki har da Dokar Laifukan Intanet (Cybercrimes Act), ba su wadatar wajen magance dukkan matsalolin da fasahar samar da bayanai da hotuna ta AI ke haifarwa ba.
Don haka, akwai buƙatar samar da fayyace kuma za a iya aiwatar da ma’anonin doka game da bidiyoyin bogi da aka ƙirƙira da gangan domin haddasa tarzoma, kawo cikas ga zaman lafiyar jama’a ko ɓata sunan ’yan takarar zaɓe.
Hukumomin da ke da alhakin kula da fasahar sadarwa, kamar Hukumar Bunƙasa Fasahar Sadarwa ta ƙasa (NITDA) da Hukumar Sadarwa ta Nijeriya (NCC), su ma suna da rawar takawa wajen tabbatar da cewa manyan kamfanonin fasaha na duniya sun ɗauki alhakin abubuwan da ake yaɗawa ta dandamalin da suke sarrafawa.
Ya kamata waɗannan hukumomi su buƙaci kafafen sada zumunta su sanya alamomin da za su bayyana cewa an ƙirƙiri wani hoto, sauti ko bidiyo ta amfani da basirar AI. Haka kuma, su samar da hanyoyin gaggawar gano labaran ƙarya da cire bidiyoyin bogi cikin mintuna, maimakon barin su su ci gaba da yaɗuwa na tsawon kwanaki.
Bugu da ƙari, ya kamata a buƙaci jam’iyyun siyasa da ke fafatawa a zaɓe su rattaba hannu kan yarjejeniyar ɗabi’a ta amfani da kafafen sadarwa na zamani. Duk jam’iyyar da ta karya yarjejeniyar kuwa, ya kamata a ɗauki matakin da doka ta tanada a kanta.
Fasahar AI na iya zama wata babbar hanya ta bunƙasa rayuwar bil’adama, amma ’yan siyasar da ba su da kishin gaskiya za su iya amfani da ita wajen tayar da hargitsi da haddasa ruɗani.
Muna ganin cewa bai kamata a yi kunnen uwar shegu da gargaɗin da Shugaban Majalisar Dattawa ya yi ba. ƙarfafa dimokuraɗiyya da tabbatar da ɗorewarta na buƙatar ’yan ƙasa su amince da wasu muhimman bayanai na gaskiya, tare da haɗa kai wajen yin tir da duk wani nau’in tashin hankali da tsoratarwa da ke barazana ga tsarin zaɓe.
Saboda haka, wajibi ne INEC ta samar da ingantattun matakan kariya daga ƙaryar da aka ƙirƙira ta amfani da AI, domin kare dimokuraɗiyyar Nijeriya daga yaudara da gurɓata sahihancin bayanai da wannan fasaha za ta iya haifarwa.
