Shekaru 66 da samun ’yanci: Kasancewar Nijeriya ɗaya babbar nasara ce, inji Kubura Ibrahim

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano

Shugabar Jam’iyyar Matan Arewa ta ƙasa, Hajiya Kubura Ibrahim ɗankanni, ta bayyana cewa kasancewar Nijeriya ƙasa ɗaya, duk da ƙalubalen da ta fuskanta tsawon shekaru 66 da samun ’yancin kai, babbar nasara ce da ya kamata ’yan ƙasar su yaba tare da ƙara ƙoƙarin tabbatar da haɗin kai da zaman lafiya.

Hajiya Kubura ta bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da manema labarai a makon da ya gabata, inda ta yi tsokaci kan nasarorin da Nijeriya ta samu tun bayan samun ’yancin kai a ranar 1 ga Oktoba, 1960.

Ta ce idan aka yi la’akari da irin ƙalubalen da ƙasar ta fuskanta a tarihi, waɗanda suka haɗa da Yaƙin Basasa, rikice-rikicen siyasa da kuma tashe-tashen hankula na ƙabilanci, kasancewar ƙasar a dunƙule wuri guda har zuwa yau wani babban abin alfahari ne.

A cewarta, duk da bambance-bambancen addini, ƙabila da al’adu da ke tsakanin al’ummar ƙasar, Nijeriya ta ci gaba da kasancewa ƙasa ɗaya, lamarin da ta ce yana nuna muhimmancin haɗin kai da fahimtar juna wajen gina ƙasa mai ɗorewa.

Hajiya Kubura ta kuma bayyana cewa tun bayan samun ’yancin kai, Nijeriya ta samu ci gaba a fannoni daban-daban, ciki har da ilimi, kiwon lafiya, aikin gona da samar da ababen more rayuwa.

Ta ce an gina makarantu na firamare, sakandare da manyan makarantu a sassa daban-daban na ƙasar, yayin da aka samu bunƙasar cibiyoyin kiwon lafiya da sauran ayyukan raya ƙasa.

Shugabar ta ƙara da cewa waɗannan ci gaba sun taimaka wajen ƙara yawan mata masu ilimi, tare da buɗe musu ƙofofin samun muƙamai a hukumomin gwamnati da sauran manyan wuraren yanke shawara a matakai daban-daban na mulki.

Ta ce mata sun samu ƙarin damar shiga harkokin shugabanci da bayar da gudummawa wajen ci gaban al’umma idan aka kwatanta da shekarun baya, duk da cewa akwai sauran ƙalubalen da ya kamata a magance domin ƙara faɗaɗa wannan dama.

Hajiya Kubura ta kuma yaba wa tsofaffin shugabannin ƙasa da na jihohi bisa gudummawar da suka bayar wajen raya Nijeriya tun daga lokacin samun ’yancin kai zuwa yanzu.

Ta yi nuni da gudummawar tsoffin gwamnonin Jihar Kano, ciki har da marigayi Audu Bako da marigayi Abubakar Rimi, waɗanda ta ce sun taka rawa wajen samar da ayyukan ci gaba a jihar.

A cewarta, ayyukan gine-gine, hanyoyi, makarantu da madatsun ruwa da gwamnatoci daban-daban suka samar sun taimaka wajen inganta rayuwar al’umma da bunƙasa tattalin arziƙi.

Ta ce ya kamata ’yan Nijeriya su riƙa duba irin nasarorin da aka samu tare da amfani da su a matsayin ginshiƙi na tunkarar ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta a halin yanzu.

Da ta juya kan matakan da ya kamata a ɗauka domin samun ƙarin ci gaba, Hajiya Kubura ta yi kira ga ’yan ƙasa da su ƙara kishin kansu, al’ummominsu da kuma ƙasarsu baki ɗaya.

Ta jaddada cewa samun ci gaba mai ɗorewa yana buƙatar haɗin kai, gaskiya da amana, tare da jajircewar kowane ɗan ƙasa wajen bayar da gudummawa ga ci gaban ƙasa.

Ta kuma buƙaci shugabanni a dukkan matakan mulki da su sauke nauyin da ke kansu ta hanyar tabbatar da adalci, samar da zaman lafiya da kuma gudanar da ayyukan gwamnati bisa gaskiya da riƙon amana.

Hajiya Kubura ta ƙara da cewa ya kamata talakawa su jajirce wajen neman sana’o’in dogaro da kai da kuma riƙe su da gaskiya da amana, tana mai cewa haɗin gwiwar shugabanni da al’umma shi ne ginshiƙin samun ci gaba da inganta rayuwar jama’a.

Ta bayyana fatanta na ganin ’yan Nijeriya sun ƙara fahimtar muhimmancin zaman lafiya da haɗin kai, domin ci gaba da gina ƙasa mai albarka wadda kowa zai amfana da damarmakinta.

By ukarofi

Leave a Reply