Shettima ya buƙaci ’yan Arewa su goyi bayan tazarcen Tinubu a 2027

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Mataimakin Shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya buƙaci shugabannin Arewa da al’ummar yankin su haɗa kai wajen marawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya domin sake zaɓensa a babban zaɓen shekarar 2027, yana mai cewa babu abin da ya kamata yankin ya ji tsoron ci gaba da mulkin gwamnatin.

Shettima ya bayyana hakan ne ranar Litinin, lokacin da ya karɓi wata tawaga daga ƙungiyar Arewa for Tinubu (A4A), wata cibiyar tunani da ke aiki wajen neman goyon bayan sake zaɓen Tinubu, wadda ta kai masa ziyarar ban girma.

Ya bayyana cewa sake zaɓen Tinubu zai samar da damammaki wajen ci gaban Arewa da inganta rayuwar al’ummarta, yana mai kira ga shugabannin yankin da su haɗa kai wajen tallafa wa manufofin gwamnatin.

“Mu haɗa kai a matsayin al’umma, mu yi aiki domin ci gaban yankinmu da bunƙasar rayuwar mutanenmu ta hanyar sake zaɓen wannan gwamnati. Muna amfana, kuma akwai sauran damammaki da za mu ci gaba da amfana da su daga wannan gwamnati,” in ji shi.

Mataimakin Shugaban ƙasar ya bayyana cewa Arewa ta amfana da naɗe-naɗe, ayyukan raya ƙasa da shirye-shiryen gwamnatin Tinubu, yana mai cewa gwamnatin na ƙoƙarin kammala manyan ayyukan more rayuwa a sassa daban-daban na ƙasar.

Ya kawo misalin Bankin Noma na Nijeriya, wanda ya ce ya bayar da rancen kuɗi har naira biliyan 450 ga manoma ƙanana 700,000 a faɗin ƙasar, inda kusan kashi 70 cikin 100 na waɗanda suka amfana suke daga Arewa.

Shettima ya kuma tabbatar wa shugabannin yankin cewa Shugaba Tinubu yana da ƙauna ga Arewa, tare da aniyar ci gaba da aiwatar da ayyukan da za su taimaka wajen ci gabanta.

Ya gode wa mambobin ƙungiyar A4A bisa goyon bayan da suke bai wa Shugaban ƙasa, sannan ya buƙace su da su ƙara ƙaimi wajen wayar da kan jama’a da tattara goyon baya a matakin mazabu, unguwanni da ƙananan hukumomi a faɗin Arewa gabanin zaɓen 2027.

Tun da farko, Darakta Janar na Arewa for Asiwaju, kuma tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Abubakar Badaru, ya bayyana cewa ƙungiyar ba za ta sassauta ƙoƙarinta ba har sai ta taimaka wajen ganin an sake zaɓen Tinubu.

Badaru ya ce ƙungiyar ta shirya yin hulɗa da shugabannin addinai, ciki har da malaman Musulunci da na Kiristanci, da sauran manyan ’yan Nijeriya domin bayyana musu dalilan da suka sa take ganin ya dace a sake zaɓen haɗin gwiwar Tinubu da Shettima a 2027.

Ya bayyana cewa ƙungiyar ta riga ta fara tattaunawa da wasu fitattun mutane, kuma kwamitin amintattunta na shirin ci gaba da ganawa da su domin ƙarfafa goyon bayan da ake samu.

Badaru ya ƙara da cewa ƙungiyar na taimaka wa Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban ƙasa (PCC) ta hanyar gudanar da ayyukan wayar da kai da tattara goyon baya a matakin tushe, domin bai wa kwamitin damar mayar da hankali kan manyan tsare-tsaren yaƙin neman zaɓe.

Ya ce: “Muna kuma tallafa wa PCC a duk abin da take buƙatar mu yi a matakin ƙananan ayyuka, domin su na da manyan tsare-tsare da suke gudanarwa. Mu kuma muna son mu mai da hankali sosai kan hulɗa da jama’a a matakin ƙananan hukumomi da mazabu.”

Shi ma Shugaban Kwamitin Amintattun ƙungiyar, kuma tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, ya bayyana cewa ƙungiyar, wadda ta yi aiki wajen neman nasarar Tinubu a zaɓen 2023, a shirye take ta sake yin irin wannan ƙoƙari a zaɓen 2027.

Shekarau ya ce ƙungiyar ta riƙa ganawa da gwamnonin Arewa da sauran masu ruwa da tsaki domin tattauna hanyoyin haɗin gwiwa da gano matakan da za su taimaka wajen cimma manufarta.

Ya kuma bayyana cewa an kammala shirye-shiryen kafa cikakken sakatariyar ƙungiyar domin inganta ayyukan gudanarwa, tare da samar da ofisoshin daraktoci da masu kula da jihohi. Ya ce tsarin zai taimaka wajen tattara rahotanni, nazarin abubuwan da ke faruwa da kuma isar da umarni ga mambobi.

A yayin taron, Shekarau ya gayyaci Mataimakin Shugaban ƙasa, Kashim Shettima, domin ƙaddamar da ginin ofishin ƙungiyar a hukumance.

Daga cikin waɗanda suka halarci taron akwai tsoffin gwamnonin Jihar Filato, Cif Joshua Dariye da Sanata Simon Lalong; tsohon Gwamnan Jihar Taraba, Fasto Jolly Nyame; tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello; tsohon Gwamnan Jihar Katsina, Barista Ibrahim Shehu Shema; da tsohon Gwamnan Jihar Bauchi, Malam Isa Yuguda.

Sauran waɗanda suka halarta sun haɗa da Mai Ba Shugaban ƙasa Shawara kan Manufofi da Haɗa Ayyuka, Hajiya Hadiza Bala Usman; Shugaban Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA), Birgediya Janar Buba Marwa (mai ritaya); da manyan jami’an gwamnati tare da mambobin kwamitin amintattu da sakatariyar ƙungiyar A4A.

Taron ya nuna shirin ƙungiyar na faɗaɗa hulɗa da shugabannin siyasa, na addinai da na al’umma, tare da ƙarfafa tsarin tattara goyon baya a matakin tushe a faɗin Arewacin Nijeriya gabanin zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

By ukarofi

Leave a Reply