
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya fitar da sunayen sababbin kwamishinonin ƙasa guda huɗu da wasu biyu a matsayin kwamishinonin zaɓe na shiyya domin maye wasu gurabe a Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC). Kakakin Shugaban ƙasa Bayo Onanuga ne ya sanar da haka a ranar Juma’a, 16 ga Oktoba, 2026, cikin wata takarda da ya fitar.
Wannan naɗi zai tabbata be bayan Majalisar Dattawa ta tantance tare da tabbatar da su a muƙaman yayin da Shugaban ya buƙaci a cike guraben da ake da su a INEC gabanin zaɓukan 2027.
A sabon naɗe-naɗen, an sake naɗa Dakta Bala Bila a matsayin kwamishinan da ke wakiltar Arewa ta Gabas a wani karo. Haka kuma, Fadar Shugaban Ƙasar ta naɗa Farfesa Mustapha Aliu a matsayin sabon kwamishinan ƙasa da ke wakiltar Arewa ta Yamma, inda zai maye gurbin Farfesa Abdullahi Zuru.
Sannan, an zaɓi Bashir Muhammed Umar ya maye gurbin Farfesa Muhammad Adamu a matsayin kwamishinan ƙasa mai wakiltar Arewa ta Tsakiya.
Tinubu ya bayar da sunan Misis Oluwatoyin Babalola, wadda ita ce kwamishinar shiyya (REC) a Jihar Osun a matsayin sabuwar kwamishinar ƙasa mai wakiltar kudu maso Yamma. Babalola zai maye gurbin Farfesa Cornelius Ajayi, wanda wa’adinsa zai ƙare a ranar 24 ga Oktoba, 2026.
Mutane biyun da shugaban ƙasar ya naɗa a matsayin sababbin kwamishinonin shiyya sune Babban Sakatare mai ritaya, Dakta Samuel Akinjide Akinleye, wanda zai wakilci Jihar Ekiti, da Zahradden Basiru Sanusi, daga Jihar Jigawa, wanda zai wakilci Farfesa Sa’idu Ahmed Ɓaɓura.
Shugaba Tinubu ya kuma buƙaci Majalisar Dattawa da ta hanzarta aikin tabbatarwar bisa la’akari da babban zaɓen da ke tafe da aka tsara gudanarwa a Junairu.
