Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Sojoji da haɗin gwiwar jami’an tsaro na CWC da mafarauta sun sami nasarar ceto mutane 27 da shanu shida daga hannun ‘yan bindiga a ƙaramar hukumar Sabuwa.
Kwamishinan cikin gida da tsaro Dr Nasiru Mu’azu Ɗanmusa ya fitar da sanarwar haka sai dai yace ‘yan bindigan suka harbe wani tsoho ɗan shekara 70 har lahira.
Waɗanda ‘yan bindigan suka sace yawancin su Mata, ƙananan yara da tsaffi amma dukkan su sojoji sun sami nasarar ceto kuma sunan nan a sansanin sojoji a garin Machika ana duba lafiyar su.
Dr Nasiru Ɗanmusa ya bayyana cewa ‘yan bindigan su 40 ƙarƙashin jagorancin Kachalla Alhaji Bawa Kabir sun kai hare hare ga wasu alummomi sai sojoji da sauran haɗin gwiwar jami’an tsaro ceto mutane 27 da shanu shida da ‘yan bindigan suka sace a Tashar Bawa bayan ɗauki da daɗi.
Haka kuma sojoji sun tare hayar da ‘yan bindigan suke wucewa zuwa sansanin su a dajin Madaci a ƙoƙarin su na kamo maharan.
Kwamishinan ya bada tabbacin cewa gwamnatin Katsina da haɗin gwiwar jami’an tsaro sun tashi tsaye wajan ganin an kamo waɗannan miyagun mutane.
