Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamna Dikko Raɗɗa na Jihar Katsina ya roƙi al’ummar Jihar Katsina da su yafe masa bisa duk wani laifi da ya aikata masu lokacin gudanar da mulkin sa a shekara uku da rabi da suka wuce.
Raɗɗa ya yi wannan roƙon ne a lokacin da yake ƙaddamar da kwanmitin yaƙin neman zaɓen Tinubu Dikko Raɗɗa a sabon sakatariyar jam’iyar APC a Katsina.
Gwamnan wanda ya yi bayani a kan aikace aikace da ya aiwatar yace a shirye yake ya yafe wa duk waɗanda su kayi masa laifi.
Yace “na yafewa duk wanda yayi mani laifi nima ina neman yafiya ga duk wanda na saɓa masa a tsawon shekara uku da rabi ina mulkin Jihar Katsina.
Ƙaddamar da kwanmitin yaƙin neman zaɓe na Tinubu/Dikko Raɗɗa 2027 ya zama wani mataki na tunkarar zaɓe mai zuwa.
