
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Dakataccen Kwamandan Hukumar Sibil Difens (NSCDC) na Jihar Neja, Siaka Zubeiru Anirive, ya bayyana cewa mutuwar masu haƙar ma’adinai ba bisa doka ba a ofishinsu abu ne da da sun kauce wa aukuwarsa, yana mai bayar da haƙuri ga iyalansu da Gwamnatin Jihar Neja kan al’amarin.
Wannan ya biyo bayan bayanin cewa lauyan Anirive ya shawarce shi da ya saki marasa galihun da ya tsare yayin atisayen. Anirive, wanda ya bayyana al’amarin a matsayin babban kuskure, ya bayar da haƙurin ne a gaban Hukumar Bincike ta Mohammed Mohammed da ke Minna, wadda ke binciken yadda al’amarin ya faru. Tsohon kwamandan ya kuma bayyana da-na-sani kan aukuwar lamarin a lokacin da yake shugaba, yana mai cewa da sun yi ƙoƙarin kare faruwarsa.
Waɗannan kalamai na zuwa ne yayin bayar da ba’asi mai tayar da hankali kan yadda aka rasa kula da mamatan gabanin rasuwarsu yadda ya dace, ciki har da zarge-zargen cewa an yi watsi da shawarar sako su kuma wata shaidar binciken wani likita ta nuna cewa ɗaya daga cikin waɗanda aka tsaren ya riƙa yin tari mai tsanani a lokacin da ake fitar da gawarwakin mamatan daga cikin magarƙamar da aka kulle su a ciki.
Da yake jawabi a gaban hukumar binciken, Anirive ya ce ya fara aiki ne a matsayin kwamandan NSCDC na Neja a ranar 25 ga Agusta, 2025, kuma ya kasance a ofis har zuwa ranar 18 ga Satumba, 2026.
Ya bayyana cewa, jami’ansu sun gudanar da atisaye ne a wani gurin haƙar ma’adinai da ke yankin Rukunin Gidajen M.I Wushishi a Minna bayan wani rubutaccen ƙorafi a gare su daga mazauna waɗanda suka yi zargin cewa ayyukan masu haƙar ma’adinan na damun unguwarsu.
A cewarsa, ya ziyarci yankin a ranar 15 ga Satumba, 2026 kana ya umarci shugaban sashen atisayensu, ACC Joha Achagwa da ya yi aiki akan ƙorafin ‘yan unguwar. Yayin da aka tura jami’ai zuwa yankin, an kama masu haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba a ƙarƙashin atisayen, wanda aka gudanar a yammacin 16 ga Satumba. Saidai, a kashe-gari mutum 37 daga cikinsu sun rasu a ofishin hukumar. Wannan al’amari ya tayar da hankalin jama’a musamman ‘yan jihar da ma ƙasa baki ɗaya wanda ya yi sanadiyyar Gwamnatin Tarayya ta dakatar da kwamandan NSCDC na yankin da kuma umartar a gudanar da cikakken bincike kan al’amarin.
