2027: Wike ya sake koma wa gidan Fubara yayin zurfafa sulhun haɗakar Rainbow Coalition

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A ranar Lahadi Ministan Abuja, Nyesom Wike da Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara suka sake ganawa a karo na biyu a ƙarƙashin haɗakar Rainbow Coalition domin zurfafa yarjejeniyarsu ta zaman lafiya da haɗewa a manufar siyasa guda gabanin babban zaɓen 2027.

An gudanar zaman ne ta bayan fage a gidan Fubara da ke Fatakwal, wanda ya haɗa jagorori da magoya baya daga ɓangarorin biyu domin warware matsalolin bambance-bambancen da ke tsakaninsu da ƙarfafa yunƙurinsu na gabatar da murya ɗaya a zaɓen da ke tafe.

Wike ya je gidan gwamnan ne da misalin ƙarfe 4:30 na yamma, inda ya samu rakiyar wata babbar tawaga da ta ƙunshi jagororin Rainbow, ciki har da ɗan takarar gwamnan haɗakar, Kingsley Chinda da Shugaban kwamitin sulhun, Sanata Magnus Abe.

Duk da cewa ba a bayyana abin da tattaunawar zaman ya ƙunsa ba, majiyoyi sun bayyana hakan a matsayin dabarar aiki da nufin ƙarfafa sulhu, warware dukkan matsalolin da ake da su da samar da kyakkyawan shiri ga zaɓukan 2027.

By Babaji

Leave a Reply