Daga MUHAMMAD SADISU ABUBAKAR Birnin Kebbi
Gwamnatin jihar Kebbi ta ƙi amincewa da rahoton da hukumar raya al’umma ta Majalisar Ɗinkin Duniya, UNDP, ta gabatar akan jihohi masu tsananin talauci a Najeriya, saboda rahoton ya ƙunshi kura-kurai da kuma rashin adalci.
A sa’ilin taron manema labarai a Birnin Kebbi, kwamishinan yaɗa labarai da al’adu, Yakubu Ahmed Birnin Kebbi, ya ce UNDP ta yi amfanine da yadda tsohuwar gwamnati da ta gabata ta gudanarda mulki daga shekarar 2018 zuwa shekaru uku na farkon zangon mulkin Buhari.
Yakubu, musamman yaji takaicin cewar jam’iyyar ADC a irin halinta na rashin mutunci, ta na amfani da bayanin UNDP, cewar wai, Kebbi na cikin jihohi mafi talaucin rayuwar ɗan-Adam a Najeriya.
Ya ce ɗan takaran gwamnan ADC, tsohon Ministan Shari’a Abubakar Malami, ya hau kan wannan rahoton na talauci, yana murna da kekkewa cewar al’ummar jiharsa na cikin ƙunci da rashin walwala, saboda ya cimma burinsa na siyasa.
Kwamishinan ya fayyace cewar rahoton na UNDP ya yi nazari ne daga shekarar 2018 zuwa shekaru uku na zangon farko na gwamnatin Buhari, wadda Malami babban jigo ne a cikinta.
Ya ce gwamnatin jihar Kebbi mai ci yanzu, ƙarƙashin jagorancin Gwamna Nasir Idris, ta yi namijin ƙoƙarin wurin raya jihar Kebbi da kuma inganta jin daɗin rayuwar al’ummomin jihar a dukkan sassa na rayuwar ɗan-Adam, tun lokacin da ya hau karagar mulki a shekarar 2023 zuwa yanzu.
Yakubu ya yi sharhin cewar abin takaici ne ganin waɗannan mutanen da sukayi ruwa-da-tsaki, suka yaudari marigyayi tsohon shugaban ƙasa, Buhari, suka gurgunta ma shi gwamnati ta hanyar wawurar ɗimbin dukiyar jama’a daga baitul-malin gwamnati, sune a yanzu suke gabatar da kansu, cewar a zaɓe su lokacin jefa ƙuri’a, saboda neman ma kansu kariya daga irin ɓarnar da suka yi a lokacin da suke akan kujerar mulki.
A nasa jawabin, mai baiwa gwamna shawara na musamman akan wayar ma al’umma da kai, da kuma sanya su akan turba ta-gari, Ibrahim Abubakar Jombali, ya fayyace cewar gwamnatin jihar ta ƙi amincewa ne da rahoton UNDP, saboda ita UNDP tilo, ta shirya rahoton ba ta tantance gaskiyar lamarin ba, ko kuma tuntubar hukumar ƙididdiga ta Jihar Kebbi domin ta samu sahihan bayanai.
