Zamfara: Ɗan takarar gwamnan ADC ya zargi jam’iyyar da miƙa sunan wanda ba ɗan jam’iyya ba ga INEC

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Ɗan takarar gwamna na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a Jihar Zamfara, Mahdi Aliyu Mohammed, ya zargi shugabancin jam’iyyar da ƙirƙirar takardun bogi tare da canja sunansa ba bisa ƙa’ida ba gabanin babban zaɓe na 2027.

A cikin wata sanarwa da ya sanyawa hannu da kansa a yau Litinin, Mahdi ya ce ya shiga zaɓen fidda gwani na ADC a Jihar Zamfara wanda aka gudanar a ranar 22 ga Mayu, 2026 kuma ya lashe zaɓen.

A cewarsa, bayan lashe zaɓen fidda gwanin, an bashi takardar INEC Form EC9 wanda ya cika ya mayar wa jam’iyyar domin miƙa wa hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC).

Ya zargi jam’iyyar da cewa maimakon miƙa sunansa ga INEC, sai ta mika sunan wani Bilyaminu Shinkafi, wanda ya ce ba ɗan jam’iyyar ADC ba ne kuma bai shiga zaɓen fidda gwanin da aka gudanar a ranar 22 ga Mayu, 2026 ba.

Mahdi ya ce wannan dalili ne ya sanya ya garzaya kotu domin neman adalci, inda ya ƙara da cewa duk da cewa an kai wa jam’iyyar da Bilyaminu Shinkafin takardun kotu sama da watanni biyu da suka wuce, har yanzu ba su gabatar da wata kariya ba.

Ya ƙara zargin cewa wasu mutane a cikin jam’iyyar ƙarƙashin jagorancin wani tsohon babban lauyan jiha na ƙoƙarin ƙirƙirar takardu da suke shirin gabatarwa a matsayin kariya a kotu.

“Mun san cewa an tsara wasiƙun, an sanya musu baya da wata rana kuma an aike su zuwa INEC suna cewa Mista Shinkafi ya shiga zaɓen fidda gwani duk da cewa rahoton zaɓen fidda gwanin da aka samu daga INEC kuma aka riga aka gabatar a kotu kafin wannan wasiƙa da ba ta wanzu ba kuma aka sanya mata baya da wata rana ya ce akasin haka,” in ji shi.

Ya yi gargaɗin cewa idan aka gabatar da jabun takardu a kotu, za a kai rahoto ga hukumomin tsaro da suka dace, da INEC da kuma kwamitin ladabtar da lauyoyi (LPDC) kan irin waɗannan mutane da masu haɗa baki da su domin a gudanar da bincike, gurfanarwa da kuma ladabtarwa da ta dace.

Mahdi ya ce: “Jam’iyyar da ke da niyyar jagoranci bai kamata ta amince da irin wannan mummunan aikin laifi ba a ƙoƙarin saka wa mutanen da ba su shiga zaɓen fidda gwanin ba. Muna matuƙar fatan hankali da tunani mai kyau za su yi rinjaye a kowane hali.”

A lokacin haɗa wannan rahoto, shugabancin jam’iyyar ADC na Jihar Zamfara da Bilyaminu Shinkafi ba su mayar da martani kan zarge-zargen ba.

By ukarofi

Leave a Reply