Ambaliyar ruwa ta kashe mutum biyu a Nasarawa

Spread the love

Daga JOHN D. WADA a Lafia

Gwamnatin Jihar Nasarawa ta tabbatar da mutuwar mutane biyu da kuma raba ɗaruruwan mazauna gidajensu sakamakon ambaliyar ruwa mai tsanani a ƙaramar hukumar Doma ta jihar.

Kwamishinan yaɗa labarai da al’adu da yawon buɗe ido na Jihar, Dakta Nawani Aboki ne ya bayyana hakan yayin da yake yi wa manema labarai jawabi a ranar Litinin a Lafia babban birnin jihar.

Aboki ya bayyana lamarin a matsayin babban bala’in jin ƙai, yana mai cewa ambaliyar ta lalata gine-gine da gonaki da dama a cikin al’ummomin da abin ya shafa.

Ya bayyana cewa ambaliyar ruwan, wacce ta faru a yankin ci gaban Eke na ƙaramar hukumar Doma, ta shafi al’ummomi sama da 18.

“Kwanan nan an samu matsalar ambaliyar ruwa a yankin ci gaban Eke na ƙaramar hukumar Doma, inda al’ummomi sama da 18 suka shafa.

“Ba ambaliyar ruwa ta al’ada ba ce kawai, amma ambaliyar ruwa ce mai tsanani da ta faru. Mutane da yawa sun rasa matsugunansu, kuma gine-gine da dama sun lalace, ciki har da gonaki,” in ji shi.

A cewarsa Gwamna Abdullahi Sule, bayan samun rahoton lamarin, ya umarci darakta janar na hukumar ba da agajin gaggawa ta Jihar Nasarawa (NASEMA) da ya ziyarci dukkan al’ummomin da abin ya shafa, yana mai cewa hukumar na haɗa rahoton da gwamnati za ta ɗauki mataki a kai.

Kwamishinan yace shi da kansa ya ziyarci yankunan da abin ya shafa tare da shugaban ƙaramar hukumar Doma domin jajantawa waɗanda abin ya shafa da kuma miƙa ta’aziyya ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu.

Game da halin da ‘yan gudun hijira ke ciki a yanzu, Aboki ya ce mutanen da ambaliyar ta raba da muhallansu (IDPs) suna fakewa ne a cikin al’ummomin da ke kan tudu kamar Agyema, Agbachi da Rukubi a cikin ƙaramar hukumar.

Ya bayyana cewa kwararowar mutanen ya zama nauyi ga al’ummomin da suka karɓe su, yana mai jaddada cewa gwamnati ta himmatu wajen tabbatar da komawar su gida da zarar ruwan ya ja baya.

Aboki, duk da haka, ya gargaɗi ‘yan gudun hijirar da ka da su koma tukuna saboda rashin tabbas game da yiwuwar sakin ruwa daga madatsar ruwa ta Lagdo da ke Kamaru.

Yace gwamnati ta fara aiwatar da samar da tallafi da kayayyaki domin hana ɓarkewar cututtuka a yankunan da abin ya shafa.

Ya kuma yi kira ga mazauna yankunan kwarowa da su koma wuraren da suka dace don gujewa aukuwar irin wannan bala’in a yanzu.

By ukarofi

Leave a Reply