
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC a zaɓen 2027, ya yi watsi da wasu zarge-zarge da wani ɗan jam’iyyar adawa ta ADC mai suna Timi Frank ya yi na cewa Gwamnatin Nijeriya tana shirin kashe tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, Atiku Abubakar.
Manhaja ta ruwaito cewa, Kakakin yaƙin neman zaɓen APC, Dele Alake, ya bayyana zargin a matsayin babban al’amarin kuma ya ƙalubalanci Frank da ya tabbatar iƙirarin nasa ta hanyar gabatar da hujjoji a kai, yana mai kira ga hukumomin tsaro da su gayyace shi domin ya bayar da hujja don kare iƙirarin.
A wata sanarwa, Dele Alake ya ce matsayin zargin da buƙatar gaggawa da ta bai wa rai kariya su suka sa ya zama wajibi Frank ya kawo hujja daga ɓangarensa domin taimaka wa hanzarta fara bincike kan al’amarin. Ya ce, wajibi ne a mu’amalanci dukkan wata sahihiyar barazanar kisa da muhimmanci ba tare da la’akari da bambance-bambancen siyasa ba. “Mun yi watsi da wannan iƙirari da babbar murya cewa fadar shugaban Nijeriya ko kwamitin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar APC na da hannu a wani yunƙuri na halaka tsohon Maitaimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar ko wani jigon adawa,” inji sanarwar.
Alake ya kuma yi watsi da rahotannin da ke cewa an janye jami’an tsaron da aka ɗora wa alhakin kula da bai wa tsohon mataimakin shugaban ƙasar tsaro, yana mai bayyana kalaman a matsayin tsagwaran ƙarya. A cewarsa, Atiku na cigaba da samun tsaro daga jami’an hukumomin ‘yan sanda da DSS.
Saɓanin abin da ya kira da “ƙarya da Frank ya ƙago”, Alake ya ce a kwanan nan ne Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya umarci hukumomin tsaro da su ƙarfafa matakan tsaro akan dukkan ‘yan takarar shugaban ƙasa da abokan tafiyarsu, da ‘yan takarar gwamna da abokan tafiyarsu a sassan Nijeriya.
Ya bayyana cewa, ba a taɓa sanya wani takunkumi ba kan jami’an tsaron Atiku, sannan a matsayinsa na tsohon mataimakin shugaban ƙasa yana amfana da kariyar tsaro biyu da gwamnati take ɗaukar nauyi, inda a yanzu ma Shugaba Tinubu ya ƙara masa ƙarfin tsaro a matsayinsa na ɗan takarar shugaban ƙasa gabanin zaɓukan 2027.
A ƙarshe, Alake ya yi kira ga ‘yan takara, jam’iyyun siyasa da magoya bayansu da su kasance masu furta abin da yake gaskiya yayin magana a bainar jama’a tare da kauce wa dukkan wani abin da zai haifar da fargaba mara ma’ana acikin al’umma.
