
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Jami’in Hukumar Tsaron Fararen Hula (NSCDC) da aka fi sani da Sibil Difens da ke bakin aiki a lokacin da aka tsare masu haƙar ma’adinai a Jihar Neja, ASC Usman Isah Ndamaka, ya shaida wa hukumar binciken shari’a cewa ya ji tsoron akwai yiwuwar waɗanda aka tsare su nuna masa fin ƙarfi muddin ya buɗe musu ƙofar ɗakin da aka rufe su duk da cewa ya yi ta jin kururuwarsu gabanin mutuwar mutum 37 daga cikinsu.
An ga yadda Ndamaka ya fashe da kuka yayin bayar da ba’asi a gaban Mai Shari’a Mohammed Mohammed na hukumar binciken da ke Minna, babban birnin jihar Neja, inda ya tabbatar da kuskuren cewa da zai iya dakatar da faruwar al’amarin sannan ya kuma bayar da haƙuri ga iyalan mamatan da gwamnatin jihar Neja.
“An riga da an yi kuskure. Ina mai bayar da haƙuri ranka shi daɗe kan mutuwar masu haƙar ma’adinai a ƙarƙashin ikona. Abin takaici ne hakan ya faru a ƙarƙashin kulawata,” ya faɗa wa hukumar. Ya ƙara da cewa: “Ina cikin halin ƙunci kuma hakan ba a sonmu ba ne ya faru. Ina mai matuƙar bada haƙuri. Na tabbatar da na yi kuskure.”
Da yake bayanin yadda al’amarin ya kasance, Ndamaka ya ce waɗanda aka kama mutum 58 ne da suka haɗa da maza 33 da mata 25, inda aka garzaya da su ofishinsu, saidai iya mutum 28 zuwa 30 ne ɗakin ajiye mai laifin nasu zai iya ɗauka. Jami’in NSCDCn ya ce hukumomi sun yi ƙoƙarin raba mata da daga cikin maza ta hanyar kai su wani ofishi, saidai babu gurbi a gurin da ake yunƙurin kai su.
A cewarsa, an kawo masu laifin ne cikin tsakar dare yayin da ake zabga ruwa, lamarin da ya sa suka gagara samar da wadatattun ɗakunan ajiye su. Ya ce, yunƙurin kai wasunsu tsohon ofishin NSCDC bai yi nasara ba sakamakon manyan masu haƙar ma’adinan sun ki amince wa hakan. Ya bayyana cewa, ya yi fargabar buɗe ɗakin ne saboda tsoron kada ‘yan haƙar ma’adinan su fi ƙarfinsu shi da waɗanda suke aiki a lokacin muddin suka yi yunƙurin tserewa.
A nasa jawabin, Shugaban Sashen Binciken NSCDC CSC Sunday Oluwadare, ya bayyana wa alƙalan cewa ya tattara bayanai da gudanar da bincike kan waɗanda aka kama kuma ya ƙwace waɗansu ababen zargi a tare da su yana mai nadamar kurakuransa kan al’amarin.
Ana sa ran sakamakon binciken hukumar shari’ar ya fitar da ainihin bayanan waɗanda suke da alhaki kan mutuwar masu haƙar ma’adinai ba bisa doka ba su 37 a hannun Sibil Difens na Neja, wanda ya auku a ranar 17 ga Satumba, 2026.
