Sanata Yari da Gwamna Idris sun ce a bar ɓangaren Kudu ya kammala shekara takwas kan mulki

Spread the love

Daga MUHAMMAD SADISU ABUBAKAR Birnin Kebbi

Darekta-Janar na majalisar yaƙin neman zaɓe na shugaban ƙasa na APC, Sanata ABDULAZIZ Abubakar Yari, ya yi muwafaƙa da Gwamna Nasir Idris na Jihar Kebbi, cewar a kyale ɓangaren Kudancin ƙasarnan ya cika shekara takwas akan karagar mulki daidai da yadda tsarin karɓa-karɓa na zama shugaban Najeriya, ya gindaya.

Wannan na cikin jawabai da su kayi a fadar mai nartaba Sarkin Gwandu da ke Birnin Kebbi.

Ittifaƙan, sun buƙaci al’ummomin Arewa maso Yamma da ɗaukacin Arewacin Najeriya su jefa ma Shugaba Bola Ahmed Tinubu ƙuri’arsu tururu a zaɓen shugaban ƙasa da za’ayi a ranar 16 ga watan Janairu 2027

Sanata Yari da sauran wakilan majalisar yaƙin neman zaben shugaban ƙasa, sun ta fi Fada ne da nufin samun tubarruki da kuma addu’oin Sarakuna.

Sarakunan da sukayi masu marhabin a Fadar ABDULLAHI Bin Fodio da ke Birnin Kebbi, sune, shugaban majalisar sarakuna ta Jihar Kebbi, kuma Mai Martaba, Sarkin Gwandu Alhaji Muhammadu Iliyasu Bashar, da kuma mataimakin shugaba, kuma Mai Martaba Sarkin Kabin Argungu, Alhaji Sama’ila Muhammadu Mera, da kuma, Mai Martaba Sarkin Yauri, Dakta Muhammadu Zayyanu ABDULLAHI, da kuma Mai Martaba Sarkin Zuru, Alhaji Muhammadu Sanusi Mikhailu, ‘Gomo na Uku’.

Da yake ma sarakunan jawabi, Gwamna Nasir Idris, ya bayyana cewar Kebbi, jiha ce ta APC-SAK wadda ta jajirce wurin bai wa shugaba Tinubu goyon baya ya koma mulki zango na biyu, saboda haka zasu zuba masa ƙuri’a chakwakwa a zaɓen 2027.

Gwamnan ya yi bayanin cewar abubuwan da jama’a ke gani akasin haka a kafofin sada-zumunci na social media, zuƙi-ta-malle-ce, karereyi ne, a yi watsi da su.

Kwamred Idris ya ce APC ta kafu daram-dam a jihar Kebbi, ya mai cewar ai Darekta-Janar shi-da-kanshi ya ga hujja, yadda jama’a suka yi tururuwa suka yi marhabin da wakilan majalisar yaƙin neman zaɓen, da nufin nuna soyayya ga shugaba Tinubu wanda ya yi hoɓɓasa wurin kawo ma al’ummar jihar Kebbi romon dimokraɗiyya na inganta rayuwarsu.

Gwamnan ya ce Arewa ta share shekara takwas akan mulki, saboda haka, bisa turba ta gaskiya da adalci da wanzar da ‘yan’uwantaka tsakanin al’umma, a bar sashen kudu shima ya kammala shekara takwas yana mulki daidai da tanaje-tanajen tsarin karbar-karba.

Kwamred Idris ya yabama Sarakuna dangane da yadda suke nuna goyon baya da ɗa’a da haɗin-kai ga gwamnatin APC mai-ci-yanzu a matakin tarayya da kuma na Jihar.
Ya yi tambihi garesu da su wanzar da wannan karimci.

Shi ma a nasa jawabin mai-kama-da-wannan, darakta-janar na yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC, Sanata Abubakar Yari, ya jaddada cewar a da-fa ma ɓangaren Kudu baya, shima ya ci moriyar shekara takwas akan mulki.

Sanata Yari ya ce an san Arewa mai son adalci ne, sannan kuma ganin yadda mutanen Kudancin ƙasar nan sukayi hankuri, suka yarda Arewa ta yi zango biyu tana mulkin Najeriya, kuma a yanzu shekara uku ne kachal Arewa Maso Yamma ta sauka daga mulkin Najeriya.

Ya ce wajibine su ma ‘yan Arewa suyi riƙo da gaskiya da adalci, ayi ma kudu adalci ta kammala shekara takwas, saboda haka, a jefa ma Shugaba Tinubu ƙuri’a ya zarce akan mulki.

Sanata Yari ya ce yin haka shine ginshiƙin zaman lafiya da wanzuwar haɗin-kai, domin shine tafarkin samu ƙasaitacciyar ƙasarmu Najeriya.

Darakta-Janar ya ce wakilan kwamitin na zaɓen shugaban ƙasa na APC, sun kai ziyara Fada ce mai daraja domin jaddada mubaya’arsu ga sarakuna da kuma neman tubarruki da kuma neman addu’arsu dangane da aikin da ke gaba, na zaɓen 2027.

Ya ce sarakuna su ne uwayen al’umma, saboda haka a matsayin ‘yan-kwamitin masu biyayya, sun zo fada ne domin girmama masarauta.

Sanata Yari ya ce ‘yan siyasa sun yi na’am da matsayin sarakuna na dattijai masu shiryar da al’umma tafarkin alkhairi da kuma gangamin zaman lafiya da haɗin-kai na jama’a.

Ya ce Shugaba Tinubu ya nuna ƙwazo wurin raya Najeriya, ya kawo bunƙasar tattalin arziki da walwalar al’umma da haɓɓaka aikin gona da gina hanyoyi da sauran manyan ayyukan gine-gine.

Yari ya ce Tinubu bai yi ƙasa a gwiwa-ba wurin kawo ɗauki ga jama’ar Najeriya ta hanyar samar masu da kuɗaɗen kula da rayuwarsu ta yau da kullum da kuma sana’oi.

Darakta-Janar ya ce matsalolin tsaro, al’amarine da gwamnati mai ci yanzu ta gada, kuma gwamnati ta ɗora fifiko wurin kawo ƙarshen shi.

Ya ci gaba da cewar shugaba Tinubu ya tura ƙarin manyan makamai da dakarun tsaro masu ƙwarewa zuwa wuraren da ake fama da ta’addanci, musamman a Arewacin Najeriya domin kawo ƙarshen rashin tsaro, kuma ana samun nasara.

Darekta-Janar ya yaba ma Gwamna Nasir Idris dangane da yadda ya raya jihar Kebbi, da kuma yadda ya yi gangamin jama’a suci gaba da bai wa Shugaban ƙasa Tinubu goyon baya.

Da yake maida jawabin a madadin sauran Sarakuna, Mai Martaba Sarkin Gwandu, Alhaji Muhammadu Iliyasu Bashar, ya yi addu’ar samun nasarar shugaban ƙasa da kuma Gwamna Nasir Idris a zaɓen 2027.

Ya ce jama’a su zaɓi Tinubu saboda ya sanshi, a matsayin mai sauƙin-kai, abokin-kowa mai fara’a da mutane.

Sarkin ya ce kafin ya zama shugaban ƙasa, Tinubu ya zo Kebbi ya Shugabanci taron ƙaddamar da littafin tarihin rayuwar shi Sarkin Gwandu, Muhammadu Iliyasu Bashar.

Mai Martaba ya ce wannan karimci da Tinubu ya yi, girmamawane ga Sarauta, da kuma ƙarfafa haɗin-kan ‘yan Najeriya.

Ya ce, Shugabanci nauyi gare shi, saboda haka ‘yan Najeriya su jinjina ma Tinubu ganin yadda yake bada himma wurin inganta rayuwar jama’a.

Sarkin Gwandu ya buƙaci Shugaba Tinubu ya yi waiwaye baya, domin nazarin inda aka fito da nufin sha-ta mafificiyar hanya kuma sahihiya na ɗorewar ci gaban al’ummomin Najeriya, tare da yalwa da kuma walwala.

By ukarofi

Leave a Reply