Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano
Kimanin mutane 500 masu fama da larurorin ido ne za su ci gajiyar shirin bayar da magunguna, gilashin ido da tiyata kyauta da wata ƙungiya mai suna Women Capacity Builders Association (WOBA) ta shirya, tare da haɗin gwiwar ƙungiyoyin VisionSpring da See Well Organizations, a yankin ƙaramar Hukumar Dawakin Kudu.
An tsara gudanar da shirin ne na tsawon kwanaki biyar.
Da yake yi wa manema labarai bayani kan makasudin shirin, Sakataren Shirye-shirye na ƙungiyar WOBA ta ƙasa, Malam Isma’il Sani Barkun, ya ce an shirya gudanar da aikin ne saboda matsalolin ido da ke addabar al’umma. Ya ce ƙungiyar ta ga ya dace ta shirya wannan shiri domin duba lafiyar masu fama da matsalolin ido. Ya bayyana cewa za a ba wasu magunguna, wasu kuma a ba su gilashin ido, yayin da waɗanda ake buƙatar yi wa tiyata za a tura su asibitoci domin yi musu aikin kyauta.
Barkun ya ƙara da cewa shirin haɗin gwiwa ne tsakanin ƙungiyarsa da wata ƙungiya mai suna VisionSpring da See Well Organizations, wadda za ta riƙa biyan wani kaso na kuɗin magani ko aikin da aka yi wa marasa lafiya.
Ya ce ana sa ran duba aƙalla marasa lafiya 500 a yankin, inda za a riƙa duba su kullum daga safe har zuwa yamma a kowace rana ta shirin. Ya kuma yi kira ga waɗanda suka amfana da shirin da su yi amfani da magungunan da aka ba su yadda ya dace domin kula da lafiyarsu. Bugu da ƙari, ya gargaɗi marasa lafiya da su guji amfani da magunguna ba tare da samun shawarwari daga ƙwararrun ma’aikatan lafiya ba.
A nasu ɓangaren, wasu daga cikin waɗanda aka tattauna da su bayan an duba su kuma aka ba su magunguna, Malama Sa’adatu Yahaya Ahmad da Malam Dahiru Inuwa, sun yaba wa ƙungiyoyin bisa wannan aikin alheri da suka kawo musu na ɗaukar nauyin magunguna da tiyata kyauta.
