Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano
Alhaji Yakubu Haruna, Shugaban ƙungiyar Masu Mallakar Motocin Sufuri, reshen kasuwar tashar Sunga ta Kano, wato Road Transport Employers Association of Nigeria (RTEAN), ya bayyana cewa kowace mota da ke tasha tana samar da aikin yi ga mutane 30 a kullum, tun daga lokacin da aka yi mata lodi har ta tashi zuwa wani gari.
Shugaban ƙungiyar RTEAN, Alhaji Yakubu Haruna, ya bayyana hakan a wannan lokaci, inda ya ce ƙungiyar na taka muhimmiyar rawa wajen samar wa matasa aikin yi. Ya ce hakan na rage wa gwamnati nauyi, tare da taimakawa wajen bunƙasa tattalin arzikin ma’aikata da iyalansu, da na jiha da ƙasa baki ɗaya.
Ya ƙara da cewa ƙungiyar RTEAN na da kyakkyawar alaƙa da hukumomin kasuwa da sauran hukumomi masu ruwa da tsaki a harkokin sufuri, irin su Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta Kano (KAROTA) da sauransu.
Bugu da ƙari, ya ce ƙungiyar na aiki tuƙuru wajen sayen ƙasar ciko domin cike duk wani wuri da ake buƙatar ciko a tashar, don tabbatar da cewa komai na tafiya yadda ya kamata. Ya ce gudunmawar da ƙungiyar ke bayarwa ba za ta ƙidayu ba.
A ƙarshe, ya yi kira ga mambobin ƙungiyar da su riƙa bin doka da oda, musamman ƙa’idojin mallakar motoci da dokokin tuƙi. Ya kuma buƙace su da su riƙa kyakkyawar mu’amala da al’umma da kuma bayar da taimako a duk inda ya dace, yana mai cewa irin waɗannan halaye ne suka samar wa ƙungiyar kyakkyawan suna a tsakanin al’umma.
