
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Yayin da ya rage saura ‘yan kwanaki a gudanar da taron karrama wasu fitattun ‘yan ƙasa na Henna Ball & Tozali People’s Award na 2026, wanda shi ne karo na 8, shirye-shirye sun yi nisa daga ɓangaren kamfanin Tozali Media Group mai shiryawa.
Za a gudanar da taron ne a ranar 31 ga Oktoba, 2026 a babban ɗakin taro na Los Angeles Event Centre da ke Ahmadu Bello Way a Birnin Tarayya Abuja, wanda za a fara daga ƙarfe 6:00 na yammaci. Sannan taken taron na wannan shekara shi ne “Empowering Survivors. Restoring Hope,” inda za a karrama wasu sanannun ‘yan ƙasa bisa jagoranci, gadon al’ada, ƙirƙira, waƙa, harkokin al’umma da kira ga ayyukan jinƙai.
Ana sa ran wannan taro da aka saba yi a kowace shekara zai haɗa fitattun mutane daga fannoni da suka haɗa da gwamnati, cibiyoyin al’adu, kasuwanci, taimakon al’umma, jarida, nishaɗi da ƙungiyoyin al’umma domin karrama muhimman gudumawara da ‘yan ɓangarorin suka bayar don ci-gaban ƙasa da nasarori acikin al’umma.
Daga cikin waɗanda aka gayyata a taron na bana akwai fitattun ‘yan ƙasa kamar haka:
“Dr. Mrs Maryam Sani Abacha — Former First Lady of the Federal Republic of Nigeria; Mother of the Day.
- Alhaji Bashir Mohammed Dalhatu, Wazirin Dutse — Chairman and Chief Host.
- Honourable Mohammed Idris Malagi — Minister of Information and National Orientation; Special Guest of Honour. Honourable Aisha Ismail — Former Minister of Women Affairs; Keynote Speaker.
- His Imperial Majesty, Ooni Adeyeye Enitan Ogunwusi, Ojaja II — Royal Father of the Day. Haj. Turai Umar Yar’Adua — Tozali Woman of Distinction Award.
- His Imperial Majesty, Ooni Adeyeye Enitan Ogunwusi, Ojaja II — Tozali Royal Leadership Award.
- Dr. Dauda Lawal, Executive Governor of Zamfara State — Governor of Excellence Award.
- Dr. Agbu Kefas, Executive Governor of Taraba State — Champion of Women Empowerment Award.
- General Christopher Gwabin Musa (Rtd.), OFR — Outstanding Security Leadership Award.
- Honourable Abdussamad Dasuki — Distinguished Legislative Award.
- Fatima Shinkafi — Excellence in Public Service Award.
- Sir Ahmadu Bello Memorial Foundation — Humanitarian Excellence Award.
- Stonetech Square Limited — Excellence in Business Innovation Award.
- Senator Datti Yusuf Baba-Ahmed — Business Leadership recognition.
- Nasiru Danu — Humanitarian Icon recognition.
- Mohammed Bashir Dalhatu — Lifetime Achievement recognition.
- Nazeeru Sarkin Waka
- Hausa guy
- Amal Hassan
- Isa Bello Ja” da dai sauransu, kamar yadda jaridar NewsPointNigeria ta wallafa.


