Mutum biyar sun rasu yayin hatsarin motar tawagar Gwamna Bago da ta makaranta a Neja

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Aƙalla mutum biyar ne suka rasu a ranar Litinin a lokacin da wata mota daga cikin tawagar motocin Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago ta yi kiciɓis da wata mota, lamarin da ya haifar da mummunan hatsari a tsakaninsu.

Manhaja ta ruwaito cewa, al’amarin ya auku ne a yankin Gidan Mangoro da ke garin Minna, wanda ya haɗa wata Toyota Hilux da ke ɗauke da Darakta-Janar na Gidan Gwamnatin Neja, Dauda Chikuba da wata mota mai ɗauke da ɗaliban Jami’ar Fasaha ta Tarayya da ke Minna. Huɗu daga cikin ɗaliban sun rasu a nan take tare da direban motar gwamnatin da ke ɗauke da daraktan.

Haka kuma, Manhaja ta gano cewa al’amarin ya faru ne a lokacin da tawagar motocin gwamnan ke koma wa Minna, yayin ita kuma motar da ta yi jigilar ɗaliban ta nufi yankin Bida. Wani shaida ya ce tawagar gwamnan tana kan hanyar dawowa ne daga ziyarar ta’aziyya a fadar Sarkin Nufawa (Etsu Nupe) kuma Shugaban Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Jihar Neja, Alhaji Yahaya Abubakar, bisa rasuwar ‘Sagi Nupe’, Hajia Aisha.

Tuni dai aka garzaya da daraktan gidan gwamnatin zuwa asibiti domin masa magani yayin da aka tafi da gawarwakin waɗanda suka rasu zuwa wani waje da ba a bayyana ba. “Taho mu gama aka yi. Mun gano cewa tawagar tana gudu ne sosai a lokacin da al’amarin ya faru. Mummunan hatsari ne,” inji wani shaida.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Neja, SP Wasiu Abiodun ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce ana kan bincike a kai. Saidai bai bayyana sunayen waɗanda suka rasu ba. “Hatsarin ya auku ne a wannan safiyar kuma muna bincike a kai,” inji Abiodun.

By Babaji

Leave a Reply