Kafin da bayan rasuwar Sheikh Masussuka

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUH’D da ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Babu shakka rahoton da ya tayar da hankali ga al’ummar Jihar Katsina da Arewa da ma Nieriya bakiɗaya shine na samun labarin cewa, wasu ’yan-bindiga-daɗi da suka halaka fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Yahaya Ibrahim Masussuka, mai shekaru 47, tare da abokinsa, Adamu Abubakar, a garin Dutsin-Ma.

Lamarin ya faru ne a daren ranar Litinin, 26 ga Oktoba, 2026, da misalin ƙarfe 7:30 na dare, a daidai ƙofar gidan marigayin da ke cikin garin Dutsin-Ma. Binciken da Blueprint Manhaja ta gudanar ya gano cewa, maharan su biyu ne da suka iso akan babur suna ɗauke da ƙananan bindigogi, watp ‘pistol’a turance. A cewar ɗan uwan marigayin, Alhaji Surajo Abbas Zaradden, maharan sun yi lallaɓe ne kusa da gidan Sheikh ɗin kafin su buɗe masa wuta. “Sun zo a lallaɓe ba tare da wata magana ba suka buɗe masa wuta. Mutane sun taru da hayaniya, amma maharan sun riga sun gudu,” in ji Zaradden.

Hajiya Fatima Masussuka, matar marigayin ta farko, wacce ta zanta da manema labarai a gidan mijinta, ta bayyana yadda lamarin ya faru a idonta. Ta ce, “Yana shirin zuwa wajen karatu ne tare da almajiransa. Na raka shi har ƙofar gida, sai na koma ciki, saboda ya manta jakarsa. Ban gama shiga ba sai na ji ƙarar harbe-harbe guda huɗu. Da na fito cikin firgici, sai na tarar da mijina kwance cikin jini.”

Sakataren marigayin, Dakta Muhammad Mustapha Haruna, shine wanda aka kira a waya a lokacin, inda ya garzaya da Sheikh ɗin zuwa asibiti, inda likita ya tabbatar da cewa ya rigaya ya rasu.

Marigayi Sheikh Yahaya Ibrahim Masussuka ɗan asalin Jihar Katsina ne ta fuskar mahaifi, amma ya taso a garin Masussuka dake ƙaramar hukumar Ningi ta Jihar bauchi. Sai dai ya zaɓi Dutsin-Ma da ke Jihar Katsina a matsayin matsuguninsa na shekaru da dama. Ya shahara a faɗin Arewacin Najeriya, saboda karatuttukansa da suka dogara kan tafsirin Al-ƙur’ani zalla. Yana daga cikin malaman da ke ganin cewa Al-ƙur’ani kaɗai ya wadatar, kuma yana sukar wasu hadisai da yake ganin sun saɓa wa ƙur’ani da asalin koyarwar Manzon Allah (SAW).

Haka kuma wannan kisa na zuwa ne daidai da lokacin da Marigayi Sheikh Masussuka ya kammala shirye-shiryen gudanar da babban taro na zaman lafiya a birnin Katsina. Kamar yadda bayani ya gabata, taron da zai haɗa da Musulmi da Kirista, zai gudana a filin wasa na Muhammadu Dikko ne.

Wannan aƙida ta ƙur’aniya zalla ake ganin ta saka shi cikin cece-kuce da malaman ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bid’a wa Iƙamatus Sunnah, wacce aka fi kira da Izaka, da kuma na Salafiyya. Harkar ta kai ga an taɓa ɗaure shi na tsawon watanni tara a kurkuku. A watan Afrilu na shekarar 2024 ya kafa gidan rediyo da talabijin mai suna ƙur’an Tɓ da kuma makarantar Masussuka International School a Dutsin-Ma.

Duk da cece-kucen aƙida, an san shi da kira ga zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin Musulmi da Kirista. A watan Yuni na 2025, ƙungiyar Network for Good Goɓernance and Transparency ta karrama shi da lambar yabo ta Jakadan Zaman Lafiya.

A watan Nuwamba na shekarar 2025, Gwamnatin Jihar Katsina ta gayyaci Sheikh Masussuka gabanta, bayan da wasu ƙungiyoyin addini suka kai ƙorafin cewa, karatunsa na cin mutuncin hadisan Manzon Allah (SAW). A lokaci guda, shi ma Sheikh ɗin ya kai kuka ga gwamnati cewa, wasu mutane na zagin sa da yi masa barazanar kisa a kafafen sada zumunta. Gwamnatin ta miƙa batun ga Majalisar Masarautar Katsina da kuma kwamitin malamai, domin sasanta ɓangarorin biyu. Kisan nasa ya zo ne kafin a kammala sulhun.

Tun daren ranar Litinin ji kaɗamn bayan kisan , Rundunar ’Yan Sandan Jihar Katsina ta tabbatar da faruwar lamarin, kamar yadda jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, DSP Abubakar Sadiƙ Aliyu, ya fitar, inda ya ce, Baturen ’Yan Sanda na Yanki (DPO) na Dutsin-Ma ya jagoranci tawagar ’yan sanda zuwa wurin da abin ya faru nan take bayan samun labari.

Sanarwar ta ƙara da cewa, Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar, CP Ali Umar Fage, ya bayar da umarnin tura ƙarin jami’an ‘Operation’ da na ‘Tactical’ zuwa yankin, domin farautar maharan da suka tsere.

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya bayyana alhininsa mai zurfi kan kisan. A cikin sanarwar da babban sakataren yada labaransa, Ibrahim Kaula Mohammed, ya fitar, gwamnan ya bayyana marigayin a matsayin “malami mai kishin zaman lafiya da haɗin kai tsakanin al’umma.”

Ya tabbatar da cewa, gwamnatin Katsina za ta yi cikakken bincike, domin gano waɗanda suka aikata wannan ɗanyan aiki. “Waɗanda suka aikata wannan mummunan aiki dole ne a hukunta su. Ina kira ga jami’an tsaro su gudanar da cikakken bincike, kuma Ina kira ga al’ummar Dutsin-Ma da su kwantar da hankalinsu,” in ji Gwamnan.

Haka zalika, Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ƙungiyar kare hakkin ɗan adam ta Amnesty International sun yi Allah-wadai da kisan, inda Amnesty ta tunatar da cewa, marigayin ya daɗe yana fuskantar barazana ga rayuwarsa.

Shi ma Hon Bubba Kaita, ɗan takarar Gwamnan Jihar Katsina a ƙarƙashin jam’iyyar adawa ta ADC, ya yi ta’aziya da iyalai da mabiya da al’ummar ƙaramar hukumar Dutsinma da Jihar Katsina kan rashin da aka yi. Ya zargi gwamnatin Katsina da gazawa wajan samar da tsaro ga al’ummar jihar tare da kira ga jami’an tsaro su gudanar da cikakken bincike, don gano waɗanda suka aikata wannan ta’addanci.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, ‘yan sanda sun ce ba a kama kowa ba, amma ana ci gaba da bincike. Sai dai mai sharhi kan al’amuran tsaro, Barista Audu Bulama Bukarti, ya ƙungiyar Boko Haram, ta wani sautin murya da Bulama ya saki, ƙungiyar Ansaru ta zargi Shikh Masussuka da adawa da Musulunci. Sai dai ba ta bayyana laifi da ya aikata ba.

Amma sai dai ɗaya daga cikin ɗalibin Marigayi Sheikh Masussuka, wato Imam Abdulkarim Abdulrasheed, wanda aka fi sani da Imam Rasheed, ya musanta bayanin da Barista Audu Bulama ya yi na hunnun ƙungiyar Ansaru wajen kisan Sheikh Masussuka.

A wani faifan bidiyo, Imam Rasheed ya zargi Audu Bulama da neman siyasantar da lamarin domin a canza lamarin kisan. “Ba mu san Ansaru ba, ba mu da wata alaƙa da ita, ba mu da matsala da ita, kuma ba su nemi muƙabala da mu ba,”Inji shi.

Ya ce, kuskure da Bulama ya fara yi shine da faɗin ranar Talata da lamarin ya faru a maimakon Litinin. “Tambaya ga Bulama, ina ya samo bidiyon wanda ya yi magana kuma ya sunan wanda ya yi kisa kuma a ina suka haɗu suka ba shi bidiyon,”inji Imam.

Imam ya yi zargin cewa, waɗanda suka yi yunƙurin kashe Malam Masussuka an san su masu magana ta yanar gizo ne, a cewarsa babu abinda ba su faɗa ba. ɗalibin ya ce, irin wannan siyasa da farfaganda mun san ana so a canza magana ne.

Sai Imam Abdulkarim ya yi kira ga hukumomin tsaro da su tsananta bincike na gano waɗanda suka yi wannan aika-aika, kuma ya yi kira ga mutanensu su kwantar da hankali kamar yadda aka san su a matsayin Peace Ambassadors, Allah zai mayar masu da haƙƙinsu.

Ya kuma sanar da ranar Juma’a za a yi jana’izar Sheikh Masussuka a fadar Sarkin Katsina, kuma taron zaman lafiya da aka shirya za a yi kafin rasuwarsa yana nan daram a ranar Asabar mai zuwa za a gudanar da taron a garin Katsina. “Muna sa ran isowar duk waɗanda muka gayyato a nan Nijeriya da ƙasashen sa ran duniya bakiɗaya,” inji Imam Abdulkarim.

’Yan uwa da maƙwabta na Marigayi Sheikh Yahaya Ibrahim Masussuka sun bayyana yadda abubuwa suka kasance a sa’o’in ƙarshe na rayuwarsa, kafin wasu ’yan bindiga su halaka shi a gaban gidansa da ke Dutsin-Ma, Jihar Katsina, a yammacin ranar Litinin.

An kashe malamin tare da abokinsa, Adamu Abubakar, a wani hari da ake zargin ‘yan ƙungiyar masu tsattsauran ra’ayin addini ta Ansaru ta ɗauki alhakin kai wa. Kisan ya jefa iyalansa, almajiransa da abokan hulɗarsa cikin alhini.

Sa’o’i kaɗan kafin a kashe shi, ya halarci wani zaman makoki a gidan surukinsa, inda ’yan uwa da sauran masu yi wa iyalin ta’aziyya suka taru. A cewar waɗanda suka halarci zaman, malamin ya yi magana kan tabbataccen zuwan mutuwa ga kowane mutum, tare da jaddada muhimmancin zaman lafiya da kyautata alaƙa tsakanin al’umma. An ce ya tunatar da masu ta’aziyyar cewa, bambancin launin fata, ƙabila, ƙasa ko matsayi a cikin al’umma bai kamata ya zama sanadin rarrabuwar kawuna ba, domin a ƙarshe kowa zai koma ga Allah.

Wani mazaunin yankin, Murtala Narega, wanda ya san yadda sa’o’in ƙarshe na malamin suka kasance, ya shaida wa Daily Trust cewa, Sheikh Masussuka ya yi amfani da zaman makokin wajen kira ga mutane da su fahimci juna, maimakon su mayar da bambance-bambancen da ke tsakaninsu sanadin gaba. “Ya tunatar da mu cewa Allah ne ya halicci mutane cikin bambance-bambance, amma hakan bai kamata ya zama dalilin rarrabuwar kawuna ko ƙiyayya a tsakaninsu ba,” inji Narega.

Ya ƙara da cewa, malamin ya yi magana kan tabbatacciyar mutuwa ba tare da la’akari da dukiyar mutum, matsayinsa ko irin yanayin rayuwarsa ba. “Ya gaya mana cewa wannan duniyar wurin zama ce na ɗan lokaci, kuma kowa zai koma ga Allah a ƙarshe. Ya shawarce mu da mu yi amfani da lokacin da muke da shi wajen aikata alheri da yi wa bil’adama hidima,” inji shi.

Narega ya ce, kalaman malamin sun ƙara zama masu taɓa zuciya bayan rasuwarsa, sa’o’i kaɗan bayan ya yi wannan wa’azi. “Babu wanda ya yi zaton za mu shiga jimamin rasuwarsa jim kaɗan bayan mun saurare shi yana magana kan mutuwa. Kalmominsa sun zauna a zukatanmu, domin ya tunatar da mu cewa rayuwa ba ta dauwama, amma ba mu san cewa ajalinsa ya kusa ba,” inji shi.

Bayan kammala taron, an ce Masussuka ya koma ɗakin da yake gudanar da wa’azinsa a gidansa, inda ya saba gabatar da karatun addini ga mabiyansa ta kafafen sadarwa na intanet.

Matar marigayin, Hajiya Fatima, ta ce mijinta ya tunatar da ita game da kaɗaita Allah kafin ya fita daga gida a ranar da aka kashe shi. Ta ce jim kaɗan bayan fitarsa, sai ta ji ƙarar harbe-harbe, kafin daga bisani ta samu labarin cewa an kashe shi. “Mijina ya yi mini magana game da kaɗaita Allah kafin ya fita daga gida. Jim kaɗan bayan ya fita, sai na ji kamar harbe-harbe guda huɗu. Daga nan ne na samu labarin cewa an kashe shi,” inji matar marigayin. Ta ƙara da cewa, “Ina roƙon Allah Ya gafarta masa kura-kuransa, Ya kuma sanya shi cikin Aljannatul Firdausi.”

Yanayin kisan ya bar ’yan uwa da abokan malamin cikin tambayoyi da dama, musamman kan ko waɗanda suka kai harin sun san motsinsa ko kuma sun daɗe suna sa ido a kansa kafin su kashe shi. Rasuwarsa ta kuma sake jawo hankalin jama’a kan saɓanin fahimtar addini da ya kasance tsakanin malamin da wasu malamai da ƙungiyoyin addini sakamakon wasu koyarwarsa.

Mataimakin marigayin, Muhammadu Sabi’u, ya ce, al’ummar yankin sun shiga cikin firgici da alhini sakamakon kisan. “Mun shiga mamaki da baƙin ciki matuƙa saboda rasuwarsa, amma muna da yaƙinin cewa Allah zai ba shi Aljannatul Firdausi,” inji Sabi’u.

Ya ce an shawarci dubban mabiyan malamin da su kasance cikin natsuwa da zaman lafiya a wannan lokaci mai wuya, tare da guje wa kalamai ko matakan da ka iya ƙara tayar da hankali a tsakanin jama’a.

Wani makusancin malamin, Bello ɗanwaire, wanda ya ce shine ya taimaka wajen ƙaura da Masussuka daga Bauchi zuwa Dutsin-Ma a shekarar 1988, ya bayyana marigayin a matsayin mutum mai mutunci wanda yake girmama mutane ba tare da la’akari da addinin da suke bi ba.

ɗanwaire ya ce, ɗaya daga cikin manyan darussan da ya koya daga dangantakarsa da malamin shi ne girmama mutuncin ɗan Adam. Ya bayyana cewa, Masussuka ya kasance yana nuna ta hanyar ɗabi’unsa cewa bambancin addini bai kamata ya hana mutane mutunta juna da fahimtar juna ba. Malam Yahaya Bani Adam, wanda ya koyar da Masussuka, shi ma ya yi kira ga almajiran malamin da su ci gaba da kyautata mu’amala da sauran jama’a.

Ya bayyana marigayin a matsayin mutumin da rayuwarsa ta cancanci a yi koyi da ita, sannan ya gargaɗi mabiyansa da su guji kalaman da za su iya tunzura mutane ko haddasa tashin hankali.

Bani Adam ya ce, hukunci na ƙarshe na Allah ne, yayin da binciken kisan ya rataya a wuyan hukumomin da abin ya shafa. Ya ƙara da cewa, iyalan marigayin da almajiransa na jiran izinin da ya dace daga gwamnati kafin su kammala shirye-shiryen binne shi.

Shi ma fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya yi kira ga jama’a da su kwantar da hankulansu, su kuma bar hukumomin da abin ya shafa su ɗauki matakan da suka dace. Gumi ya yi wannan kira ne cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook da aka tabbatar da sahihancinsa, sa’o’i kaɗan bayan kisan. Ya bayyana lamarin a matsayin babban kuskure da ka iya haddasa rikici a tsakanin al’ummar Musulmi.

Malamin ya yi gargaɗin cewa akwai yiwuwar wasu su yi amfani da lamarin wajen haifar da ruɗani da rarrabuwar kawuna a tsakanin Musulmi. Saboda haka, ya buƙaci jama’a da kada su ɗauki doka a hannunsu. Ya kuma kawo ayoyin Alƙur’ani domin ƙarfafa kira ga natsuwa, yana mai gargaɗin mutane da su guji matakan da ka iya haddasa tarzoma, su kuma miƙa batutuwan da suka shafi tsaro ga hukumomin da suka dace.

Yayin da yake ambaton aya ta 83 a cikin suratun Nisa’i, Gumi ya jaddada muhimmancin mayar da al’amuran tsaro da abubuwan da ke haddasa fargaba ga waɗanda ke da alhakin gudanar da su, maimakon yaɗa bayanai ba tare da bincike ba.

Ya kuma ambaci aya ta 63 a cikin suratun Nur, yana mai gargaɗin cewa wasu ayyuka na iya haifar da fitina da mummunan sakamako. Gumi ya yi addu’ar samun zaman lafiya da kawo ƙarshen rikici a tsakanin al’ummar Musulmi.

Salon koyarwar addinin Musulunci na Sheikh Masussuka bai rasa jawo muhawara ba. An san shi da mayar da hankali kan Alƙur’ani, musamman hanyar tafsirin Alƙur’ani da Alƙur’ani, wato fassara wata aya ta hanyar amfani da wasu ayoyi daga cikin littafin mai tsarki. Matsayinsa kan wasu ruwayoyin Hadisi ya jawo saɓani da wasu malamai da ƙungiyoyin addini.

A halin da ake ciki, ana sa ran gudanar da taron da ƙungiyar ‘Yan Alƙur’ani Zalla da ƙungiyar Samar da Zaman Lafiya (ƙur’anic Belieɓers Harmony for Peace Initiatiɓe) ta shirya ƙarƙashin jagorancin Malam Masussuka a ranar Asabar kamar yadda aka tsara, duk da kisan shugabanta. Bayanai sun nuna cewa taron zai mayar da hankali kan addu’o’in zaman lafiya, inganta tsaro da kuma gudanar da zaɓe ba tare da tashin hankali ba.

An ajiye gawar malamin a Asibitin Koyarwa na Tarayya da ke Katsina domin gudanar da binciken gawar kafin binne shi a yau Juma’a. Kisan Masussuka ya jefa al’umma da mabiyansa cikin jimami tare da haifar da tambayoyi kan dalilin kai harin da kuma ainihin waɗanda suka aikata shi. Duk da saɓanin fahimtar addini da ya kasance tsakaninsa da wasu malamai, abokan hulɗarsa sun yi kira ga jama’a su kwantar da hankulansu, tare da barin binciken kisan a hannun hukumomin da abin ya shafa.

By ukarofi

Leave a Reply