
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Fim ɗin Kakanda, wanda Toka McBaror ya bada umarni, ya yi nasarar lashe kyautar Dikalo na fim mai dogon zango mafi kyau a taron bajekolin finafinai na Festival International du Film Panafrican (FIFP).
An fitar da sakamakon ƙarshe ne ga jama’a a ranar 26 ga Oktoba bayan kammala taron a ranar 25 ga Oktoba.
Kakanda ya lashe kyautar Gwarzuwar Jaruma ga Mairama Amina Shehu, wanda ya sa ya zama fim mafi kyau da ya shiga taron. Haka kuma an bai wa Wale Ojo kyautar Gwarzon Jarumi bisa fim ɗin Lights Out (Extinction des feux) wani fim ɗin Kamaru da Enah Johnscott ne mai bada umarni.
Game da shirye-shirye da suka faru a gaske, an bai wa fim ɗin Kongo da Faransa, Mud and Blood (Le sang et la boue) kyautar karramawa a matsayin mafi kyau a ire-irensa, wanda Jean-Gabriel Leynaud ne furodusa.
Fim ɗin Madagascar, What Remains of Me Here da Darcy Andriamendrikaindrindra, wanda na Belgian-Malagasy ne, ya lashe kyautar shirin gaske mai gajeren zango mafi kyau. Till Death (Jusqu’à la mort) da Yana Bille-Chung (US) ne darakta, ya lashe kyautar mafi gajertar fim.
A rukunin ƙirƙirarrun finafinai, kwamitin jagororin taron ya karrama The Colour of Exile na Azlarabe Alaoui, wanda aka yi a Faransa da Moroko. An kuma karrama The Talent of Achille na Daniel Nlandu Nganga, fim ɗin Guadeloupean da Amilcar an Miguel Eek, da aka yi tsakanin Cape Verde, France, Portugal, Spain da kuma Sweden daga cikin finafinan gaske masu dogon zango.
Wannan taro dai yana karrama masu ruwa da tsaki a harkar finafinan Afirka da ma ƙasashen wasu nahiyoyi, sannan ganin yadda furodusoshin Kakanda da Lights Out suka samu karramawa a taron bajekolin Faransan, gagarumar nasara ce Turai.
