
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa ya samu gamsuwa bayan kammala ibadar Umara a Makka, Saudiyya.
Shugaban ya faɗi haka ne jim-kaɗan bayan kammala ibadar, wadda ya bayyana ta a matsayin damar samun kusanci ga Allah (SWT) da kuma yi wa Nijeriya addu’ar samun nasarori. “Al’amari ne na samun kusanci ga ubangiji a gare ni da Nijeriya. Ina godiya ga Allah bisa wannan dama,” inji shi.
Ya ce, ya ɗauki matakin ne bisa ƙaunar al’umma da kuma ƙoƙarinsa ga aikin hidima a gare su, yana mai bayyana yaƙininsa ga ikon Allah kan wasu muhimman al’amura. Tinubu ya kuma yi addu’a domin samun zaman lafiya, haɗin kai da farin ciki a Nijeriya. “Mun yi addu’a ga ƙasarmu. Mun yi addu’a ga kowa ya rayu bisa haɗin kai, farin ciki da imani da Allah madaukaki,” inji shi.
Sauran waɗanda suka yi tafiyar tare da Shugaban kamar su Hamshaƙin Attajiri Abdul Samad Rabi’u da Gwamna Babagana Umara Zulum sun bayyana ziyarar a matsayin mai muhimmanci musamman ganin yadda suka samu damar tafiya tare da shugaban.
Shi ma Mai taimaka wa Tinubu kan harkokin yaɗa labarai, Tunde Rahman ya ce Tinubu na zuwa ibadar akai-akai ne domin neman kariyar Allah a tsawon shekaru. Ya tunatar da lokacin da ya raka Tinubu zuwa Umara a shekarar 2016. Sannan shugaban ya je ibadar Umara gabanin zaɓen 2023.


