Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau
Tsohon ɗan takarar Gwamna kuma jigo a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a Jihar Zamfara, Dr. Sani Abdullahi Shinkafi, ya sha alwashin cewa ba zai janye daga takarar kujerar Sanatan Zamfara ta Arewa ba saboda kowa, komai matsayinsa.
Ya yi wannan bayanin ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a gidansa da ke Gusau ranar Asabar.
Shinkafi ya bayyana cewa babu wani ɗan siyasa a jihar ko a matakin ƙasa na jam’iyyar APC da zai iya hana shi tsayawa takarar kujerar.
Jigon na APC ya yi kira musamman ga tsohon Gwamnan Jihar Zamfara kuma Sanata mai wakiltar Zamfara ta Yamma, Sanata Abdulaziz Yari Abubakar, da sauran manyan masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a jihar, da su ba da damar gudanar da sabuwar zaɓen fidda gwani na Shiyyar Sanatan Zamfara ta Arewa, bisa ga hukuncin kotun ɗaukaka ƙara da ke zamanta a Sakkwato.
A cewar Shinkafi, kotun ɗaukaka ƙara ta soke zaɓen fidda gwani da aka gudanar a baya kuma ta bayar da umarnin a gudanar da sabo, umarnin da ya ce dole ne a mutunta shi domin adalci, daidaito da zaman lafiyar siyasa.
“Babu wani babban ɗan siyasa, musamman Sanata Abdulaziz Yari ko wani a APC, da zai iya tilasta ni na janye takarar Sanatan Zamfara ta Arewa,” in ji shi.
A cewarsa, dole ne a gudanar da zaɓen fidda gwani kamar yadda kotun ɗaukaka ƙara da ke zamanta a Sakkwato ta yanke hukunci.
Ya jaddada cewa hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) da shugabancin jam’iyyar APC na ƙasa dole ne su tabbatar da gudanar da sahihin zaɓen fidda gwani na gaskiya, adalci da kuma bayyana gaskiya.
Ya ƙara da cewa zaɓen fidda gwani na gaskiya shi kaɗai ne zai iya tabbatar da zaman lafiyar siyasa a Zamfara ta Arewa.
Shinkafi ya yi gargaɗin cewa duk wani yunƙuri na murɗe ko rusa tsarin zai haifar da sakamako a lokacin zaɓe.
“Idan muka gano cewa akwai yunƙurin hana mu adalci a zaɓen fidda gwani na kujerar Sanata a Zamfara ta Arewa kamar yadda kotun ɗaukaka ƙara da ke zamanta a Sakkwato ta yanke, to mu ma za mu ɗauki mataki a akwatunan zaɓe a zaɓukan da ke tafe, ba tare da la’akari da wanda abin ya shafa ba,” in ji shi.
Ya bayyana cewa kujerar Sanatan Zamfara ta Arewa ta ci gaba da zama abin ce-ce-ku-ce a cikin jam’iyyar APC a Jihar Zamfara, inda ɓangarori daban-daban ke fafatawa don karɓe ragamar jam’iyyar gabanin babban zaɓen 2027.
Shinkafi ya sake jaddada biyayyarsa ga jam’iyyar APC, amma ya dage cewa dole ne a mutunta dimokuraɗiyya ta cikin gida da hukunce-hukuncen kotu domin jam’iyyar ta ci gaba da zama da haɗin kai da ƙarfi gabanin zaɓuka.
