Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Rundunar ‘yan sanda a Katsina sun tabbatar da kama mutane uku bisa zargin kai wa motocin APC hari a garin Ƙanƙara da ke kan hanyar su ta zuwa yaƙin neman zaɓen 2027 a Jihar.
Jami’in hulɗa da jama’a na ‘yan sanda a Katsina DSP Abubakar Sadiq Aliyu ya fitar da sanarwar haka ya ce lamarin ya faru ne bayan da ayarin motocin Gwamna Dikko Raɗɗa sun wuce zuwa garin Faskari inda za su gudanar da kamfen.
Ya bayyana cewa bayan da suka wuce sai wasu matasa da ake zargi ‘yan bangar siyasa suka tare hanyar zuwa Faskari a kauye yankara suka kai ta jifar motocin da sauran ayarin da duwatsu tare da ƙona hotunan ‘yan takara.
DSP Abubakar ya ƙara da cewa ‘yan bangan sun ƙona wata mota ƙirar Sharon da ta lalace bayan da aka ajiye ta a gefen hanya.
Ganin haka haɗin gwiwa na jami’an tsaro ƙarƙashin jagorancin DPO na Faskari suka suka kawo ƙarshen hare haren matasan.
Waɗanda aka kama sun haɗa da Garba Sha’aibu , Salmanu Ibrahim da Nasifi Hussaini waɗanda suna hannun ‘yan sanda.
Kwamishinan ‘yan sanda CP Ali Fage ya gargaɗi ‘yan bangar siyasa da su guji neman tada fitina a yayin gudanar da yaƙin neman zaɓe da sauran bukukuwan siyasa yace “duk waɗanda aka samu da haddasa fitina doka zata yi aiki a kan sa,”Inji CP Fage.
Kwana biyu da suka wuce irin wannan hare hare aka kaiwa ayarin motocin APC a garin Malumfashi nan take yan Sanda suka kama mutane 14.
