Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA
Wannan makon zan gabatar mu ku maƙalar da na gabatar a taron da sashen labarun yanar gizo ya shirya a Kaduna don ƙarawa juna sani wanda ya gudana ranar Litinin 26/10/2026. Ga taken darasin da na gabatar da maƙalar a kansa kamar haka: Amfani da Kafafen Sada Zumunta Wajen Yaƙi da Labaran ƙarya, ƙarfafa Haɗin Kai da Samar da Zaman Lafiya a tsakanin ƙabilu.
GABATARWA – Kafafen sada zumunta sun samo sunansu daga “social network” da waɗanda su ka ƙirƙirosu su ka yi hakan don haɗa kan mutane su yi zumunci da juna don gaisawa ko ƙulla abota tsakanin al’ummar gari daya kasa ko ma faɗin duniya. Alƙaluma sun nuna akwai mutum biliyan 8.32. Tuni kafafen sun sauya zuwa na sadarwar zamani ta yanar gizo don isar da sako cikin sauri ba tare da jiran sai an kunna rediyo, talabijin ko an jira buga jarida ko mujalla ba. Hakanan ba sai mutane ko wakilan kafafe sun aika labaru ta mota, jirgin kasa ko jirgin sama ko turawa ta gidan waya da ka iya ɗaukar fiye da sa’a 48 kafin isa tushen wallafawa ba. Kafafen sun samu saurin karɓuwa ne don yadda mutane ke samun damar ba da ra’ayinsu ba tare da an goge mu su ko an yi mu su gyara ba duk da matuƙar hatsarin hakan.
RASHIN RARIYAR TACE LABARU A KAFAFEN ZAMANI KE HADDASA YAɗA LABARUN ƙARYA
Ba kamar kafafen gargajiya da ke da rariyar tace labaru don editoci da ke duba labarin da kuma wakilan da ke rubuta labarun sun samu kwarewar aiki da bin dokoki na aikin; su na yanar gizo akasari mutane ke rejista a wayarsu ta salula su kuma rubuta abun da ya yi musu daɗi na gaskiya ne ko akasin haka kuma ba lallai da tunanin wane tasiri labarin zai yi ga zaman lafiya ko zaman tare na al’umma ba. Wasu daga kamfanonin sadarwar na da dokoki da kan sa su sauke labarun karya ko na batsa amma duk da haka masu iya shirga karya kan sakaya bayanan ta hanyar da na’ura ba ta iya ganewa. Kazalika abun da ya ke haramun a dokokin Musulunci ba lallai su ne haramun a ƙa’idojin kamfanonin ba. Wannan ya sa ya na da muhimmanci masana ilimin sadarwa masu addini su duƙufa wajen ƙirƙirar manhajojin da ke da tsarin addini kamar yadda a ka kafa bankuna masu bin ƙa’idar addini. Kafafen ka iya ɗaukar sunan HALAL SOSHIYAL, ISLAM NETWORK ko ATTAUHID da sauran sunaye masu ma’ana kamar TIKTOK na Sin/China ka iya zama TALKTRUTH.
YADDA A KE GANE LABARUN KARYA CIKIN SAUKI A MISALI 7:
1. Duk kafafen labaru na gargajiya na da shafukansu na yanar gizo don haka zai yi wuya manyan kafafe su iya yaɗa labarin ƙarya a shafukansu sai in ya zama da kuskure ba ganganci ba.
2. Idan an ga labari a wata kafa da ba a tantance sahihancinta ba kar a ɗora sai an yi bincike ko an jira wasu kafafe masu kamanta gaskiya sun kawo labarin.
3. Duk mutumin da ya rubuta labari alhali ba sunan gaskiya ba hoto ba adireshi to kai tsaye a guji labarinsa ko da zai iya zama gaskiya don hanya ce da masu makirci ke bi don yayata farafaganda.
4. A riƙa tantance hotuna da fayafayan bidiyo da a kan iya haɗawa da manhajar AI. Idan an ga hoto ko bidiyo na labari kan wasu mutane da alamu ke nuna an kala mu su sharri ne to a dau hoton ko bidiyon a tambayi AI don sanin sahihancin labarin. Haƙiƙa ta nan za a samu aƙalla tushen labarin. Kwanan nan mun binciko wani dan shigar burtu ya makala hotonsa da manhajar AI a ranar Jumma’a da masallacinmu na helkwata a Abuja. A cikin hoton nasa har da wani ɗan gayu mai hula hana sallah wanda hakan na iya jawo zargin mai nazari cewa akwai lauje cikin naɗi.
5. A guji saurin amincewa da labarun da ke fitowa daga magoya bayan ‘yan siyasa da a ke kira DATA BOYS don tabbas wasu ‘yan siyasa kan sayawa wasu matasa wayoyi masu tsada don sukar abokan hamayya.
6. Wasu masu son tara mabiya a shafukan sadarwa kan yi kwance-kwance su maka karya ta hanyar ɗaukar hoton wani babban mutum ko shahararren malami su ce ya rigamu gidan gaskiya ko jami’an tsaro sun kama shi. Da zarar ka ga wannan labari ka duba su waye masu shafin in ka lura sabbin yankar rake ne kar ka ɗorar da labarin.
7. Juya ma’anar magana ta hanyar ɗauko kaulin wani da manna hotonsa da kalamai a jiki da amfani da kaloli masu burgewa alhali labarin ba gaskiya ba ne ko an yi hakan ne don bata sunan wani musamman an fi yi wa manyan malaman addini haka. In ka ga an yi irin wannan rubutu da kaloli ka nemi faifan bidiyo ko na sauti daga shafin malamin ko shafuka da a ka amince da su don tantance gaskiya.
HAɗIN KAN ƙASA DA ƙABILU TA YAƙI DA LABARUN ƙARYA
Bayan taken Nujeriya, ƙasar na da kirari na haɗin kai a tsakanin mutane mabambanta “UNITY IN DIɓERSITY” don samun damar zama tare a ƙasar tsakanin mabiya addinai da ƙabilu daban-daban da ma waɗanda ba sa bin kowane addini. Juyin mulkin 15/01/1966 ya haddasa targade a hadin kan jama’ar Nijeriya inda wasu sojoji da akasari daga wani sashe ɗaya na ƙasa su ka yi juyin mulki da ya yi sanadiyyar kisan gilla ga Firaminista Sir Abubakar Tafawa Balewa, Firimiyan Arewa Sir Ahmadu Bello, Firimiyan kudu maso yamma Chief Ladoke Akintola da wasu sojoji ‘yan asalin Lardin Arewa. Wannan daga bisani a 1967 ya kai ga yaƙin basasa a sanadiyyar ayyana ballewa daga Najeriya da gwamnan soja na kudu maso gabar Odumegwu Ojukwu ya yi. A gurguje bayan kammala yakin mun san yadda shugaban mulkin soja na lokacin Janar Yakubu Gowon da abokan aiki su ka yi yunƙurin kawo haɗin kan ƙasa ba tare da ɓangaranci ko kabilanci ba har da ayyana ba wanda ya yi nasara a yakin sai Nijeriya “no ɓictor no ɓanƙuished”
A sabon zamanin nan wasu na neman dawo da wannan targade na aware da shiga rigar makirci ta ƙabilanci don haddasa fitina. A tsarin mulkin Nijeriya kowa na da hurumin yin addini da zama inda ya ke so ba tare da fuskantar tsangwama don bambancin addini, siyasa ko ƙabila da sauran dalilai ba. Haƙiƙa a nan dai Arewa duk wanda ya shiga rigar ƙabilanci ko ya fake da ƙalubalen tsaro wajen cusa ƙabilanci a ciki na nuna kwangilar makirci ta yaƙi da addini musamman Musulunci. Akwai masu cin zarafin malamai da nuna an daina yaudararsu da addini. In ka bincika za ka ga rubutu ne a yanar gizo kuma masu rubutun akasari na amfani da sunayen karya kuma ba hoto inda bincike na kwakwaf ke nuna ba mabiya addinin da su ke cewa an daina yaudararsu da shi ba ne. Dama ba sa cikin addinin balle a yaudare su! Shugaba Sheikh Abdullahi Bala Lau na cewa Musulmi ba za su iya korar kirista daga Nijeriya ba haka su ma Kiristoci ba za su iya korar musulmi daga Nijeriya ba . Don haka kowa sai ya girmama juna a zauna lafiya kowa ya yi addininsa. Babban taron JIBWIS da haɗin guiwar majalisar Musulunci ta duniya ta shirya a Abuja kwanan nan ya ɗau kwararan matakai wajen kyautata zamantakewa a tsakanin ‘yan Nijeriya inda manyan jami’ai daga ƙungiyar Kiristoci ta Nijeriya CAN su ka halarta da nuna gamsuwa da wannan matakin. Don haka duk mai fakewa da ƙabilanci don haddasa fitina ta addini wa inma ya na wakiltar son zuciyarsa ne ko wakilin wasu masu son wargaza salamar zaman tare ne a Arewa da Nijeriya.
KANUN LABARU MASU HATSARI GA LABARUN GASKIYA
Labari ka iya zama na gaskiya amma yadda a ka lullube shi da kalmomin kiyayya ka iya haddasa rashin fahimta. Misali akwai wani hari da a ka kai kan wani masallaci a jihar Borno a 2025 har a ka samu asarar rayuka kuma harin ya zo ne a jajiberin ranar kirsimeti. Nan wani gidan talabijin ya rubuta “A na fargabar mutane da dama sun mutu yayin da harin bom ya girgiza Maiduguri a jajiberin Kirsimeti” MANY FEARED DEAD AS BOMB BLAST ROCKS MAIDUGURI ON THE CHRISTMAS EVE.
Hakanan kan ƙalubalen tsaro sai an yi takatsantsan wajen alaƙanta hakan da ƙabilanci maimakon yaƙi da mugayen mutane daga ko ina su ke. Alaƙanta fitina da ƙabilanci kan iya ruruta fitinar ta canja salo har mutanen da ke zaune lafiya su iya komawa zaman doya da manja. Fitinar Rwanda a 1994 ta Hutu da su ka yi kisan kare dangi kan Tutsi a Rwanda babban darasi ne. Wannan fa ya auku ne bayan wani ya ƙirƙiro zayyana ‘yan Tutsi da zama kyankyasai INYENZI a yaren HUTU sai kawai masu yayata farafaganda su ka hau kafafen labaru su na zayyana TUTSI da hakan har ta kai ga kashe dan TUTSI kamar kashe kyankyaso ne kawai.
Duk inda mu ka ga wani na neman ruruta ƙabilanci ko zayyana wani mutum da mummunar siffa mu yi ma sa nasiha in Musulmi ne in kuma ba Musulmi ba ne mu nuna ma sa illar fitina in ta taso to ba lallai mai tada ita shi kansa ya tsira ba.
KAMMALAWA
Ina mai gode wa ƙungiyar JIBWIS da kwamitin soshiyal midiya don tsara wannan taro da ma wasu tarukan da a ka gudanar a baya kamar na kwanan nan a ɗakin taro na masallacin Gwallaga a Bauchi. Allah ya sakawa kowa da ya ba da gudunmawa da ma masu bi ta yanar gizo don amfanar da juna da bayanan tarukan da alheri.
