Wutar sola ta haddasa gobara a wani gida a Katsina

Spread the love

Wutar sola ta haddasa gobara a wani gida a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina

Gobara ta tashi a wani gida da ke bayan otal ɗin Jamvali a Unguwar Liyafa a jihar Katsina, inda ake zargin na’urar inverter da ake amfani da ita wajen samar da wutar lantarki ce ta haddasa gobarar.

Bayanin haka na ƙunshe cikin wata sanarwar da sashen hulɗa da jama’a na hukumar kashe gobara ta Jihar Katsina ya fitar a ranar Litinin.

Sanarwar ta ce, hukumar ta samu kiran gaggawa daga Bishir Garba da misalin ƙarfe 2:17 na rana, inda jami’an kashe gobara ƙarƙashin jagorancin Muhammad Ahmad suka isa wurin domin gudanar da aikin kashe gobarar.

Hukumar ta ce, ginin yana da gidajen zama biyu, inda kowannensu yake ɗauke da falo ɗaya, ɗakunan kwana biyu da ɗakin girki.

Wasu maƙwabtan gidan sun danganta gobarar da na’urar inverter, amma hukumar ba ta tabbatar da ainihin musabbabin gobarar ba.

Hukumar ta shawarci al’umma su riƙa amfani da ƙwararrun masu aikin lantarki wajen girka na’urorin solar da inverter, tare da amfani da kayan aiki masu inganci da na’urorin kariya daga tashin wutar lantarki domin rage haɗarin gobara.

By ukarofi

Leave a Reply