Gwamnatin Tarayya ta samar da hukuncin ta’addanci 2,512 bayan shari’o’i 11

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnatin Tarayya ta sanar da samar da hukunce-hukuncen shari’o’i masu alaƙa da ta’addanci guda 2,512 bayan shigar da ƙarin wasu ƙararraki guda 791 a zango na 11 na gurfanar da mutane da dama a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.

Kodinetan Cibiyar Yaƙi da Ta’addanci ta Ƙasa na Ofishin Mai Ba wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkar Tsaro, Manjo Janar Adamu Laka ne ya bayyana haka a ranar Talata, wanda ke nuna kawo ƙarshen zangon shari’o’in.

An gudanar da shari’o’in ne a tsakanin ranakun 15 da 17 da kuma tsakanin 22 da 24 na Oktoba, 2026. Laka ya ce zango 10 na farko na shari’o’in ya yi sanadiyyar yanke wa mutane 1,721 hukunci, yayin da na kwanan nan ya ƙara wasu guda 791, lamarin da ya kai jimillarsu 2,512. A cewarsa, an gudanar da shari’o’i 1,069 a kotuna 10 na Babbar Kotun Tarayyar.

Sakamakonsu sun haɗa da hukunci 791,waɗanda aka wanke guda bakwai, an sallami 41, an kori huɗu, an janye uku, an ɗage 211, ana aiki kan 11, yayin da kuma aka sanya guda a wani aji, kamar yadda ya bayyana.

Ya ce, ɗaya daga cikin hukunce-hukuncen da suka fi shahara shi ne wanda aka yanke hukuncin kisa kan wani ɗan Boko Haram mai suna Suleiman Abu, bisa zama mamban ƙungiyar ta’addanci da kuma shiga cikin wasu hare-hare akan kayayyakin sojoji da fararen hula, wanda ya haifar da mace-mace da manyan raunuka kan wasu.

A cewarsa, matakin ya nuna yadda fannin shari’ar Nijeriya ke ƙoƙarin tabbatar da masu hannu a ta’addanci sun fuskanci hukuncin doka. Ya ƙara da cewa, zangon na yanzu ya fi mayar da hankali kan hanyoyin samun kuɗaɗen da ake ɗaukar nauyin ta’addanci da su, inda aka samu shari’o’i 201 da kotunan ta yi hukuncin akansu.

By Babaji

Leave a Reply