Sarkin Daura ya buƙaci a riƙa yanke hukuncin kisa ga masu safarar miyagun ƙwayoyi

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Sarkin Daura Umar-Faruk Umar, ya buƙaci majalisar dokoki ta ƙasa da ta kafa dokar da za ta tanadi hukuncin kisa ga duk wanda aka samu da laifin safarar miyagun ƙwayoyi.

Sarkin ya yi wannan kiran ne a yayin wani taron wayar da kan jama’a da hukumar wayar da kan jama’a ta ƙasa (NOA) ta shirya a Daura, Jihar Katsina.

Ya kuma buƙaci ’yan majalisa su ƙarfafa dokokin da ake da su, tare da samar da hukunci mai tsauri domin daƙile safarar miyagun ƙwayoyi da shan su.

Alhaji Faruq Umar-Faruk ya bayyana aniyarsa ta tallafa wa duk wani shiri na yaƙi da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi, yana mai cewa lamarin na da matuƙar muhimmanci ga makomar Arewacin Najeriya da ƙasar baki ɗaya.

Tun da farko, jami’an NOA sun ce sun zaɓi Jihar Katsina domin gudanar da taron ne saboda matsalolin da suka shafi miyagun ƙwayoyi a yankin Arewa maso Yamma. Sun kuma yi kira ga al’umma, sarakunan gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki da su haɗa kai wajen yaƙi da matsalar.

By ukarofi

Leave a Reply