Abdul El-Sayed ya zama Musulmin farko a Amurka da ya lashe zaɓen sanata

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ɗan tsagin jam’iyyar Democrat da ke Amurka, Abdul El-Sayed ya lashe zaɓen sanatan yankin jihar Michigan, inda hakan ya sa ya zama sanata Musulmi na farko a tarihin ƙasar. Wannan nasara ta biyo bayan fafatawa mai zafi da rikice-rikicen cikin gida da dabaibaye ‘ya’yan jam’iyyar.

El-Sayed ya doke Mike Rogers ne ne jam’iyyar Republican a zaɓen, bayan jure wa hare-haren da aka riƙa kai masa a siyasance cikin har da jingina masa hannu a ta’addanci da kuma gagarumin rikici da wani ɗan jam’iyyarsa.

Rogers, wanda ya samu goyon bayan Shugaba Donald Trump, ya kiran El-Sayed da ɗan jari hujja da kuma sukar matsayarsa kan Isra’ila da kasancewarsa Musulmi.

Bayan jiran sa’o’i tare da kallon ribar dimukraɗiyya na wanzuwa a sassan ƙasar, magoya El-Sayed sun yi murna cikin dandazo a lokacin da ya hau kan mimbari domin gudanar da jawabin samun nasara.

Wannan nasara ta samu ne kwanaki kaɗan da abokin hamayyar El-Sayed, Haley Stevens ya nuna goyon bayansa ga Rogers ana gab da zaɓen.

By Babaji

Leave a Reply