NUJ za ta karrama wasu ƙwararru a taron karrama fitattun ‘yan jarida

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A halin yanzu an shirya tsaf domin gudanar da taron karrama wasu fitattu a fannin jarida a Nijeriya, wanda Sakatariyar Ƙasa ta Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Ƙasa (NUJ) ta shirya, inda daɗaɗɗun ‘yan jarida kamar su Alhaji Abdulkadir Ahmed Ibrahim (Kwakwatawa), Azubuike Ishiekwene da wasu ƙwararru suka shiga sahun waɗanda za a karrama.

Manhaja ta ruwaito cewa, taron zai karrama wasu fitattun ‘yan jarida ne waɗanda gudunmawarsu a harkar ta taimaka wajen bunƙasa lamuranta a Nijeriya. A sanarwar da Sakataren kwamitin shirya taron, Olayide Awosanya ya fitar, masu shirya taron sun ce Gwamna Sheriff Francis Oborevwori na Jihar Delta zai halarci taron a matsayin Babban Baƙo na Musamman, wanda kuma aka tsara zai gabatar da muhimmin jawabin taron.

An yi wa taron take ne da: “Strengthening Democracy Through Responsible Journalism and Good Governance,” wanda za a yi a ranar Asabar, 7 ga Nuwamba, 2026 a wani ɗakin taro da ke Abuja Continental Hotel a Birnin Tarayya Abuja.

Shugaban kwamitin, Otunba Gbenga Onayiga ya bayyana cewa, taron na bana zai haɗa ƙwararru a harkar jarida da sadarwa. Ya kuma yaba Shugaban NUJ, Kwamared Alhassan Yahaya da ‘yan tawagarsa bisa cigaba shirin, wanda ke da nufi yaba wa jiga-jigan masana harkar jarida a Nijeriya yayin da suke raye a madadin jira sai bayan ba sa duniya.

Daga cikin waɗanda za a karrama akwai Alhaji Abdulƙadir Ahmed Ibrahim, FNGE, da aka fi sani da Kwakwatawa, wanda tsohon Mataimakin Shugaban NUJ ne a daga 1990 zuwa 1997 kuma tsohon Shugabanta na Jihar Kano daga 1981 zuwa 1983. A yanzu shi ne Sakatare kuma mamba na kwamitin amintattun Majalisar Tsofaffin ‘Yan Jaridar Kano.

Sauran sun haɗa da “Chief Eric Teniola, a former Director of Press at the Office of the Secretary to the Government of the Federation; veteran journalist and former Director-General of the Federal Radio Corporation of Nigeria, Barrister Yusuf Nuhu, FNGE; Olusegun Adeniyi, Chairman of THISDAY Editorial Board; Chief Abia Onyike, a former Deputy National President of the NUJ; and Ayo Adewuyi, Executive Director of News, NTA Headquarters, Abuja,” kamar yadda NewsPointNigeria ta wallafa.

Sannan, akwai “His Royal Majesty, Oba Rotimi Obamuwagun, a former Deputy National President of the NUJ; Mukhtar Gidado, a former Deputy National President of the NUJ and Special Adviser on Media and Publicity to the Governor of Bauchi State; Hajia Tabitha Sani Kangiwa; Ignatius Nwachukwu; Mrs Toro Oladapo, a former National Chairperson of the Nigeria Association of Women Journalists (NAWOJ); and Franz Ndulue”

Sai kuma “Martins Oloja, FNGE, a former Managing Director of The Guardian Newspapers, Lagos; Azubuike Ishiekwene, FNGE, Senior Vice-Chairman and Editor-in-Chief of Leadership Media Group; Kingsley Uranta of Channels Media Group, Lagos; Olori Janet Mba Afolabi, Olori of Apomu Kingdom and Publisher of SCROLL Magazine; and Bayo Bodunrin, FNGE, of DAAR Communications, Abuja.

Haka kuma, akwai “Uzoma Livingstone Isiakpu, a former Director of Information, Imo State; Adeyinka Amosu, a former Director of Lagos Operations of the Federal Radio Corporation of Nigeria; Jubrin Bello Kwami; Ayinde Soaga, a former General Manager of NTA Minna; Sumna Sambo, Director of News and Politics Editor, ARISE NEWS TV, Lagos; and Hajia Aisha Abdullahi Jao.”

By Babaji

Leave a Reply