NIMC: Yadda za ku fitar da katin shaidar zama ɗan ƙasa a kyauta

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Kula da Harkokin Samar da Shaidar Zama Ɗan Ƙasa (NIMC) ta bayyana yadda ‘yan Nijeriya za su fitar da takardar shaidarsu ta NIN daga intanet a kyauta ta manhajar NINAuth daga manyan wayoyin hannunsu.

Hukumar ta kuma nuna hanyoyin yadda za a riƙa saukewa a wani faifan bidiyo da ta wallafa a sahihin shafinta na X, a ranar Laraba, 4 ga Nuwamba, 2026 ba tare da ziyartar cibiyoyin NIN ko biyan kuɗaɗe ga wasu wakilai ba.

A cewar NIMC, matakan sune kamar haka:

  1. Sauke manhajar NINAuth daga ɗakin Google Play Store ko Apple App Store.
  2. Buɗe manhajar akan wayarka.
  3. Danna wajen da aka wallafa “Do More with NINAuth”.
  4. Zaɓi “NIN Slip” daga zaɓin da ka gani.
  5. Kammala aikin tantancewar fuska domin tabbatar da cewa kai ne.

Daga nan ne sai a danna wajen da aka rubuta ‘Download NIN Slip’ domin saukewa da ajiye ainihin takardar NIN ɗin akan wayar, kamar yadda hukumar ta bayyana. Ta bayyana cewa, ta ɗauki wannan mataki ne domin sauƙaƙe wa al’umma hanyoyin samun katin shaidarsu da rage musu tsadar zuwa ofisoshinta.

By Babaji

Leave a Reply