Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Hedikwatar Tsaron Nijeriya ta musanta wasu rahotannin da suke cewa, an ƙulla wata yarjejeniya a ɓoye ta tsagaita wuta da ƙungiyoyin Boko Haram, Islamic State West Africa Province (ISWAP) da sauran ƙungiyoyin masu aikata laifuka, tana mai jaddada cewa, ayyukan soji kan ’yan ta’adda, masu garkuwa da mutane da sauran masu ɗauke da makamai za su ci gaba a faɗin ƙasar.
Blueprint Manhaja ta ruwaito cewa babban kwamandan sojojin ya yi wannan ƙarin haske ne a daidai lokacin da ake yaɗa rahotannin cewa Gwamnatin Tarayya ta kulla yarjejeniyar tsagaita wuta a ɓoye da ɓangaren Boko Haram ƙarƙashin jagorancin Bakura Doro, wanda ake zargin ya taimaka wajen samun ɗan kwanciyar hankali a wasu sassan Arewa maso Gabas na tsawon kusan watanni uku.
Rahoton, wanda ya dogara da bayanan wasu mutane uku da aka ce suna da alaƙa da manyan ’yan ƙungiyar Boko Haram, ya yi iƙirarin cewa yarjejeniyar ta fara aiki ne tun watan Yuni, kuma ana sa ran za a ƙara wa’adinta.
Sai dai da yake magana yayin taron haɗin gwiwa na jami’an tsaro a Abuja, Daraktan Yaɗa Labarai na Tsaro, Manjo Janar Samaila Uba, ya ce sojoji na ci gaba da matsa wa ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai lamba. Ya bayyana yawan ’yan ta’addan da aka kashe, waɗanda ake zargi da aka kama da kuma waɗanda aka ceto daga hannun masu garkuwa da mutane a ayyukan baya-bayan nan a matsayin hujjar cewa sojoji ba su sassauta ba.
“Dangane da batun ko akwai yarjejeniyar tsagaita wuta da Boko Haram, ina so in fayyace cewa babu wata yarjejeniya ta tsagaita wuta.
“Idan aka yi la’akari da ’yan ta’addan da aka kashe, waɗanda ake zargi da aka kama, mutanen da aka ceto da sauran nasarorin da aka samu a ayyukanmu, a bayyane yake cewa ba mu sassauta ba.
“Za mu ci gaba da matsa wa waɗannan ƙungiyoyin masu aikata laifuka lamba,” in ji shi.
Mai magana da yawun rundunar tsaron ya jaddada cewa ayyukan sojoji ba su takaita ga Boko Haram da ISWAP kaɗai ba, har ma sun shafi masu garkuwa da mutane da sauran ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai da ke barazana ga rayuka da tsaron ’yan Nijeriya.
Uba ya ce, “Ayyukanmu ba su takaita ga Boko Haram ko ISWAP ba. Haka kuma suna kai wa masu garkuwa da mutane da sauran masu aikata laifuka da ke ɗaukar makamai domin kai wa fararen hula hari.”
Ya gargaɗi duk waɗanda ke da hannu a ayyukan laifi cewa ko dai za a kashe su yayin halastattun ayyukan soji ko kuma a gurfanar da su a gaban shari’a.
“Duk wanda ke da hannu a ayyukan laifi da ke barazana ga rayuka da tsaron ’yan Nijeriya, ko dai za a kashe shi yayin halastattun ayyukan soji ko kuma a gurfanar da shi a gaban shari’a,” inji shi.
Da yake magana kan rahotannin cewa ’yan ta’adda na ƙaura zuwa wasu sassan ƙasar da a baya ba su cika kai hare-hare ba, Uba ya bayyana hakan a matsayin wata alama da ke nuna tasirin ayyukan soji da ake gudanarwa. Sai dai ya jaddada cewa rundunar sojin ƙasar ba ta ɗauki lamarin da wasa ba.
‘Ya ce sojoji na gano wuraren da ’yan ta’addan suka ƙaura zuwa, domin hana su kafa sabbin sansanoni a waɗannan yankuna.
Ya ce, “Kasancewar wasu daga cikinsu na barin wuraren da suka saba zama, shaida ce ta nasarorin ayyukanmu. Duk da haka, ina tabbatar muku cewa ba mu ɗauki lamarin da wasa ba.”
Uba ya kuma yi nuni da kashe wani babban ɗan ta’adda a wani daji a baya-bayan nan, a matsayin hujjar cewa ’yan ta’adda ba za su samu wurin fakewa a ko’ina cikin ƙasar ba.
Ya ƙara da cewa, “Abin da muke yi shi ne gano dukkan wuraren da muke ganin sun ƙaura zuwa, tare da ɗaukar matakan kariya tun da wuri domin hana su kafa sansanoni a waɗannan yankuna.”
Daraktan Yaɗa Labaran Tsaro ya kuma bayyana cewa sauye-sauyen da aka yi kwanan nan a tsarin tura rundunonin sojoji, ciki har da kafa sabbin rundunoni, bataliya da sassa daban-daban, an yi su ne domin cike giɓin tsaro da ƙarfafa kasancewar sojoji a yankunan da ke cikin haɗari.
Ya ce sojoji za su ci gaba da gudanar da ayyukansu domin hana ’yan ta’adda faɗaɗa ayyukansu zuwa wasu sassan ƙasar.
Da yake bayar da cikakken bayani kan nasarorin da sojoji suka samu, Uba ya ce dakarun sun gudanar da ayyukan tsaro daban-daban guda 588 a faɗin ƙasar a cikin watan Satumba da Oktoba.
Ya bayyana cewa ayyukan sun yi sanadin kashe ’yan ta’adda da ’yan bindiga 435, ciki har da fitattun kwamandoji da aka bayyana sunayensu da Ali Mandara, Abba Gajiri, Habu Ikkima, Nakif Yana Faruk, Kwamanda Gogore da Abdussamad Ohida.
Uba ya ƙara da cewa sojoji sun kama waɗanda ake zargi 809, sun samu mika wuya da son rai daga ’yan tawaye 198, sannan sun kuɓutar da mutane 717 da aka yi garkuwa da su ko aka tsare.
Daga cikin waɗanda aka ceto, ya lissafa mutum 20 da ke shirin shiga aikin yi wa ƙasa hidima (NYSC) a Owerri, Jihar Imo, da kuma wasu mutum 11 a Danko-Wasagu, Jihar Kebbi.
A cewarsa, sojoji sun kuma samu gagarumar nasara ta fuskar dabarun yaƙi a Buniyadi, Baga, Kukawa, Bittai da dajin Owo, lamarin da ya raunana hanyoyin sadarwa da ayyukan ƙungiyoyin maƙiyan.
Ya ƙara da cewa, a ƙoƙarin rusa ƙarfin waɗannan ƙungiyoyi na yaƙi, sojoji sun ƙwato makamai, alburusai, abubuwan fashewa da na’urorin fashewa da ake haɗawa da hannu (IEDs) guda 5,666, tare da wasu muhimman kayayyakin da suke amfani da su wajen gudanar da ayyukansu.
