Nijeriya ta yi asarar ganga miliyan 3.3 daga satar mai a 2025 yayin da harajin NUPRC ya faɗi da tiriliyan N2.1

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Nijeriya ta yi asarar jimillar ganga miliyan 3.33 daga satar ɗanyen mai a shekarar 2025, a watanni ukun ƙarshemta, yayin da harajin Hukumar Kula da Harkokin Gudanarwar Man Fetur ta Ƙasa (NUPRC) ya rushe da kimanin Naira tiriliyan 2.14.

An bayyana haka ne a rahoton shekara da hukumar ta fitar a ranar Alhamis, wanda ya nuna cewa harajin ɗanyen mai da gas da aka karɓa ya faɗi daga tiriliyan N12.56 a shekarar 2024 zuwa tiriliyan N10.42 a shekarar 2025.

Hakan ya nuna cewa an samu faɗuwar kuɗin harajin da take samarwa da kaso 17.03 duk da ƙare-ƙaren adadin rasitin biyan kuɗaɗen ladabtarwa a fannin gas da wasu ababe.

Bayanin da rahoton ya fitar, ya nuna cewa an riƙa samun sace-sacen mai akai-akai daga zangon huɗun ƙarshe na shekarar, a lokacin da aka samu ganga miliyan 2.19. Wannan na wakiltar kaso 65.8 na jimillar adadin gangar kuma ya ninka wanda aka samu sama da sau biyar na ganga 440,434 a ɓangaren na uku bisa haɗun ƙarshe.

A gaɓar farko ta shekarar, hukumar ta fuskanci matsalolin satar ɗanyen mai a ya kai ganga 896,471, yayin da aka rasa ganga 200,400 a gaɓa ta biyu, wanda ke nuna samu gagarumar faɗuwar kuɗin shiga da jimillarsu ya kai ganga tiriliyan 3.3.

By Babaji

Leave a Reply