
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar, ya nace akan zai cigaba da zama ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027 da ke tafe duk da hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ya soke ayyana shi a matsayin ɗan takara da jam’iyyar ADC ta yi, yayin da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) a nata gefen ta shirya nazari kan tasirin hukuncin shari’ar jam’iyyarsu.
INEC ta ce, za ta yi zama a mako mai zuwa kan duba hukuncin, inda ta ƙara da cewa ba za ta ɗauki ɓangare ba a rikicin ADC har sai ta samu tare da yin nazari kan kwafin hukuncin kotun.
Kwamishinan ƙasa na INEC kuma Shugaban kwamitin wayar da kan masu zaɓe, Mohammed Haruna, ya ce hukumar ba za ta dogara da wasu rahotannin kafafen labarai ba wajen la’akari da matsayar kotun kan al’amarin. “Ba za mu ɗauki matsaya ba har sai mun ga hukuncin da kanmu. Sai mun samu ainihin kwafin hukuncin, saboda ba ma karɓar hukunce-hukunce ko rahotannin abin da kotu ta ce… saboda akwai yiwuwar su zama ba daidai ba,” inji shi.
A cewarsa, za su yi zama akan al’amarin a mako mai zuwa. Ya kuma ce, INEC za ta bayar da haɗin kai ga umarnin kotu muddin tsagin su David Mark ya ɗaukaka ƙara kan hukuncin tare da samun izinin cigaba da gudanar da jam’iyyar ko akasin haka.
Matsayar hukumar na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan Mai Shari’a Peter Lifu na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ya soke jagorancin kwamitin riƙo na su Mark da takarar Atiku ga zaɓen 2027. Hakan ya biya bayan ƙarar da tsohon Mataimakin Shugaban Jam’iyyar na Arewa maso Gabas, Nafi’u Bala Gombe ya shigar na ƙalubalantar hanyoyin da aka bi wajen naɗa Mark da wasu a matsayin ‘yan kwamitin jagorancin ADC.
A wata sanarwa da Atiku ya fitar a ranar Juma’a, ya ce wannan hukunci ba zai sa ya ja da baya ba a takarar shugabancin Nijeriya a zaɓen na 2027, yana mai zargin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da yin amfani da matsin siyasa, labaran bogi da dabarun shari’o’i wajen kassara ‘yan adawa da fusata gasar dimukraɗiyya.
