
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaba Bola Ahmed Tinubu na fatan ganin an kammala manyan layukan dogo cikin ƙanƙanin lokaci a Arewacin Nijeriya, waɗanda suak haɗa da na Kaduna zuwa Kano da na Kano zuwa Katsina zuwa Maraɗi a Nijar, inda ake fatan ƙaddamar da su a ranar 3 ga Disambar 2026.
Manhaja ta ruwaito cewa, na Kaduna zuwa Kano mai tsawon kilomita 203, ɗaya ne daga cikin muhimman ayyukan alkhairan gwamnatin Shugaba Tinubu, wanda tuni an cimma kaso 90 na kammala aikin, yayin da na Kano zuwa Katsina zuwa Maraɗi kuma ya kai kaso 70. Ana sa ran kammala su kafin ranar 3 ga Disamba.
Wannan na ƙunshe ne cikin wata da Kakakin kwamitin yaƙin neman zaɓen takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Dele Alake ya fitar, inda ya ce hakan wani ɓangare ne da ake ƙoƙarin kammalawa da nufin inganta lamuran sufuri a sassan Nijeriya.
A cewar sanarwar, a lokacin da Tinubu ya kama aiki a 2023 aikin na Kano zuwa Maraɗi an kammala iya kaso biyar ne daga cikinsa, yayin da na Kaduna zuwa Kano kuma aka yi ƙasa da kaso 30.
Ya bayyana cewa, waɗanda ayyuka su nuna yadda gwamnatin take ƙoƙarin faɗaɗa layukan dogo na Nijeriya, wanda zai taimaka wajen haɗe shiyyoyin ƙasar da samar da yanayi zirga-zirgar fasinjoji da kayayyaki a sassan Nijeriya da ma ƙasashen maƙota.
Kakakin APCn ya ƙara da cewa aikin na Kaduna–Kano, wanda cigaba ne na Abuja–Kaduna, zai samar da haɗin layin dogo tsakanin Abuja, Kaduna, Zaria da Kano, wanda zai ƙarfafa matakan sufuri tsakanin manyan cibiyoyin kasuwanci Nijeriya, yana mai jaddada wa al’umma alƙawarin Shugaba Tinubu na kammala dukkan ayyukan ababen more rayuwa a lokacin da aka tsara su.
