KILAF 2026: Bikin bajekolin finafinan harshen Afirka a Kano ya ƙarato

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Daɗaɗɗen birnin Kano na shirin karɓar baƙuncin masu shirya finafinai, masana, masu harkokin al’adu, ƙwararru kan harkokin yaɗa labarai da masu ruwa da tsaki a masana’antun ƙirƙira daga sassan Afirka da ma ƙetare.

Za a gudanar da taron ne yayin bikin bajekolin finafinai karo na 9 wanda Shirin Bajekolin Kasuwanci Finafinan Kano na Yarukan Afirka (KILAF) na Kamfanin Movie Image Limited zai jagoranta daga ranar 10 zuwa 14 ga Nuwamba, 2026.

Wannan taro kamar yadda aka saba, zai samar da fagen ɗaukaka finafinan yarukan gida, bikin alfahari da bambance-bambancen yarukan Afirka, faɗaɗa sababbin damarmaki a harkar ƙirƙira a Afirka.

Zai gudana ne ƙarƙashin taken “The African Orange Economy: A National Approach for Optimum Utilization of Opportunities through Indigenous Languages Films.” Taken yana nuna kimar tattalin finafinan yarukan gida da rawar da ‘yan bayyana al’ada ke takawa wajen samar da ayyukan yi, ci-gaban walwala da adana lamuran tarihin da kuma faɗaɗa masana’antun ƙirƙirar Afirka.

KILAF na 2026 ya samu finafinai 659 daga ƙasashe 78, wamda ke nuna yadda ya samu karɓuwa daga matakin ƙasa-da-ƙasa da ra’ayin finafinan yarukan gida. Kwamitin alƙalancin taron ya zaɓi 78 daga ɓangarorin gasa 13 daga ƙasashe daban-daban domin karramawa.

By Babaji

Leave a Reply