
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Tsohon Kwamishinan Matasa da Wasannin Kano, Mustapha Rabi’u Kwankwaso, ya ba wa Kwamishinan Yaɗa Labaran jihar, Sanusi Bature Dawakin Tofa sa’o’i 48 na ya janye kalamansa akansa tare da bayar da haƙuri, waɗanda Kwankwason ya yi zargin ɓatanci ne a gare shi, yana mai barazanar ɗaukar matakin shari’a.
Mustapha, wanda shi ne abokin tafiyar ɗan takarar gwamnan Kano na Jam’iyyar NDC, ya bayyana haka ne a lokacin da ya yi watsi da iƙirarin cewa wai mahaifinsa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya samar da Cibiyar Gyaran Hali ta Ƙiru ne saboda shi (Ɗan Kwankwason). Ya bayyana cewa, an samar da cibiyar ne a matsayin shirin gwamnati na gyaran hali ga matasa, yana mai watsi da iƙirarin cewa an kafa ne saboda wasu dalilansa na karan kai.
Tsohon kwamishinan ya kuma yi watsi da zarge-zargen cewa ya dogara ne da mahaifinsa wajen samar kamfanonin kasuwancinsa, inda ya ce ya gina su ne ba tare da jingina da kowa ba, ciki har da masana’antar shinkafarsa.
Da yake jawabi kan halin da ya kai naɗa shi Kwamishinan Matasa da Wasannin Kano, Mustapha ya yi watsi da iƙirarin cewa an naɗa shi don hakan ya zama sanadiyyar gyaran halinsa, yana mai cewa naɗin nasa ya ta’allaƙa ne da yi wa al’umma hidima.
Ya kuma zargi Sanusi Bature da yin amfani da ofishinsa wajen kai wa ‘yan adawa farmakin siyasa a madadin sauke nauyin da aka ɗora masa na sanar da al’umma labaran harkokin gwamnati.
A ƙarshe, ɗan tsohon gwamnan Kanon ya buƙaci kwamishinan da ya janye kalamansa na zargin ɓatancin akansa tare ba shi haƙuri, iyalansa da kuma al’ummar Kano, yana mai gargaɗin ɗaukar matakin shari’a cikin kwana biyu muddin kwamishinan bai yi hakan ba.
